An fara ganin hotunan kamfen ɗin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, domin takarar shugabancin ƙasar nan a shekarar 2027 a sassa daban-daban na birnin Bauchi.
Hotunan masu taken “Kaura for President 2027,” kuma an manna su a wurare masu muhimmanci kamar, sandunan wutar lantarki da manyan tituna kamar titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da Kofar Dumi.
- Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
- Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Wani matashi mai suna Aminu Auwal, wanda ya shiga aikin manna hotunan, ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa biyu ne suka ɗauke su aikin.
“Mun fara aikin ne da misalin ƙarfe 1 na dare kuma muna fatan kammalawa yau,” in ji shi.
Ya bayyana sunan waɗanda suka ɗauki aikin da cewa su ne Ya’u Ortega da Talolo, amma ba a samu damar yin magana da su ba domin layukansu ba sa shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp