Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) a karkashin jagorancin Ibrahim Musa Gusau ta bayyana goyon bayanta ga kasar Saudiyya a kokarinta na samun tikitin daukar nauyin gasar Kofin Duniya na shekarar 2034.
Yayin da Nijeriya ke taya kasar Moroko murnar samun tikitin daukar nauyin gasar Kofin Duniya tare da Portugal da kasar Sifaniya.
- Tashar Lekki Ta Sa Kaimin Bunkasuwar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka
- Illolin Rashin Yawan Shan Ruwa Ga Dan’Adam
Gusau ya bayyana cewar suna goyon bayan kudurin kasar Saudiyya domin tanada duk wani abin da ake bukata wajen daukar nauyin gasar Kofin Duniya na 2034.
Nijeriya dai tana fadi aji a harkar kwalllon kafa a nahiyar Afirika wanda hakan ya sa take da tasiri wajen zaben wanda zai dauki nauyin gasar Kofin Duniya.