Babbar Kotun Jihar Kano ta dage shari’ar Frank Geng Quangrong, dan kasar China da ake zargi da kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya, Ummukulsum Sani mai shekaru 22 a duniya.
Kamfanin dillacin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa wanda ake tuhumar wanda ke zaune a yankin Railway a Kano, ana zargin sa da laifin kisan kai.
- AFCON 2023: An Samu Daukewar Wutar Lantarki A Wasu Yankunan Kasar Cote d’Voire Sakamakon Shan Kashi
- Sin Ta Ba Da Rahoton Fadada Shigo Da Kayayyakin Gona Da Na Abinci A Shekarar 2023
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Maris, 2024 domin yanke hukunci.
Ya kuma dage zaman biyo bayan jawaban karshe da lauyoyin masu gabatar da kara da masu kare kara, Muhammad Dan’azumi da Aisha Mahmoud suka yi.
Masu gabatar da kara sun rufe karar da ke tuhumar dan China bayan gabatar da shaidu shida a ranar 21 ga watan Disamba, 2022.
Haka kuma wanda ake kara ya gabatar da shaidu guda biyu da suka hada da likita, Dakta Abdullahi Abubakar.
A jawabinsa, wanda ake tuhumar ya shaida wa kotu cewa marigayiya Ummukulsum ta kai masa hari da wuka.
“A lokacin da nake kare kaina, Ummukulsum ta cije ni a hannu da dan yatsana kuma ta yi min rauni a ‘ya’yan maraina na,” in ji Frank.
Ana zargin dan China da daba wa marigayiyar wuka a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano, a ranar 16 ga Satumban 2022.
Masu gabatar da kara sun ce laifin, ya saba da sashe na 221(b) na dokar ‘Penal Code’.