Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Jigawa, ta kama wani yaro mai shekara 15 mai suna Yau Adamu bisa zargin kashe wani matashi ɗan shekara 19 ka rikicin gona.
Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Bala Bawa Bodinga, ya tabbatar da kama Yau Adamu daga ƙauyen Auno a ƙaramar hukumar Kafin Hausa, bisa zargin kisan kai.
- Kwankwaso Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP
- Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
A cewar hukumar, rikicin ya faru ne lokacin da Yau Adamu ya ga dabbobin Aliyu Barau, na cin amfanin gonar mahaifinsa.
Wannan ya janyo faɗa tsakaninsu.
A yayin faɗan Aliyu Barau ya jikkata sosai kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa a Asibitin Gwamnati na Kafin Hausa.
An miƙa batun zuwa Rundunar ‘yansandan Jihar don ci gaba da bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp