Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware Arewacin Najeriya wajen rabon albarkatun ƙasa.
Kwankwaso ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kano kan sauya tsarin kundin tsarin mulki.
- Majalisa Ta Ba Wa Shugaban NNPCL Awa 24 Ya Bayyana Gabanta Ko Ta Sa A Kamo Shi
- Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato
A cewarsa, gwamnatin tarayya na mayar da hankali kan ci gaban yankin Kudu, yayin da Arewa aka bar ta a baya.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya musanta kalaman Kwankwaso a shafinsa na X.
Ya ce ba a manta da Arewa ba, kuma Shugaba Tinubu na aiwatar da ayyuka a yankin.
Dare, ya ce gwamnatin na gina manyan hanyoyi a Arewa kamar hanyar Abuja zuwa Kaduna, zuwa Zariya, har zuwa Kano, da hanyar Kano zuwa Maiduguri, da hanyar Sakkwato zuwa Badagry, da kuma wasu hanyoyi da suka haɗa jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna da Jos.
A fannin lafiya, ya ce gwamnati na gyara da faɗaɗa wasu manyan asibitoci a Arewa kamar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Asibitin Koyarwa na Tarayya a Katsina, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
Ya kuma an gyara sama da cibiyoyin kiwon lafiya na guda 1,000 a yankin Arewa.
A fannin noma kuwa, Dare ya ce akwai wani shiri na Dala miliyan 158.15 da ake gudanarwa a jihohin Arewa tara domin bunƙasa harkar noma.
Haka ya ce, ana ci gaba da aikin wajen haƙo man fetur na Kolmani a Bauchi da Gombe, da aikin dam ɗin ruwa a Kano, da kuma shirin ACReSAL da Bankin Duniya ke ɗaukar nauyi domin farfaɗo da ƙasa da kuma kare muhalli a Arewa.
Ya ƙara da cewa akwai manyan ayyuka a sassan makamashi da sufuri, kamar bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna har zuwa Kano mai tsawon kilomita 614, tashar wutar lantarki ta Gwagwalada da ke Abuja, da kuma tashar hasken rana da ake shirin ginawa a Kaduna.
Har ila yau, Dare ya kafa misalin inda ya ce an fara aikin layin dogo daga Kaduna zuwa Kano, daga Kano zuwa Maradi, da kuma aikin layin dogo na Kaduna wanda aka narka kuɗi Naira biliyan 100, tare da gyaran layin dogo na Abuja.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma bayyana wasu shirye-shiryen muhalli da kasuwanci kamar ayyukan Hukumar Great Green Wall da ke yaƙi da hamada a Arewa, da shirin NEWMAP da ke magance zaizayar ƙasa.
Sunday Dare ya ce duk waɗannan abubuwa an fara su ne cikin shekaru biyu kacal a ƙarƙashin shugabancin Tinubu, kuma hakan na nuna cewa ba a yi watsi da Arewa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp