A ranar Alhamis 24 ga watan nan ne aka tantance tare da amincewa da biranen kasar Sin guda tara a matsayin biranen dausayi na kasa da kasa, yayin bude taron bangarorin da suka kulla yarjejeniyar Ramsar kan filayen dausayi karo na 15 (COP15), da aka gudanar a birnin shakatawa na Victoria Falls na kasar Zimbabwe, inda hakan ya kara adadin wadannan biranen a kasar Sin zuwa 22.
Sabbin biranen tara da aka amince da su sun hada da Chongming na Shanghai, da Dali na lardin Yunnan, da Fuzhou na lardin Fujian, da Hangzhou na lardin Zhejiang, da Jiujiang na lardin Jiangxi, da birnin Lhasa na jihar Xizang mai cin gashin kanta, da Suzhou na lardin Jiangsu, da Wenzhou na lardin Zhejiang, da kuma Yueyang da ke lardin Hunan.
Magajin garin birnin Kasane na kasar Botswana, Johane Chenjekwa, ya yaba wa kasar Sin bisa yadda ta inganta aikin kiyaye filin dausayi, yana mai cewa, Afirka za ta iya cin gajiyar hadin gwiwa da kasar Sin wajen kula da filin dausayi.
Ya kara da cewa, “Za mu sa lura mu ga abun da za mu iya koya daga gare su yayin da muke hulda da juna. Su ma suna da muradin koyon yadda muke gudanar da abubuwa a nan, don haka ana samun babbar kwarewa idan ana cudanya da juna.” (Abdulrazaq Yahuza jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp