A yanzu abun da ke bayyana a bangaren siyasa shi ne yadda rigingimu suka dabaibaye shugabancin jam’iyyun APC da PDP, duk da cewa wadanda ake rigima a kansu sun kai shekara daya a kan karagar mulkin da suke kai, shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu da takwaransa na PDP Ayiochia Ayu suna fusakantar kalubale.
Jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na kasa a watan Oktoba da ya gabata, wanda taron ya bata wa wasu da dama rai don ba su sami abun da suke bukata ba. Bayan watanni kadan, wannann abu na rashin jituwa ta kai da korar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Sencondus daga jam’iyyar.
Ayu ya zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa ta hanyar tsohuwar al’adar jam’iyyar na yin masalaha a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Ayu da manyan jami’an jam’iyyar 19 daga cikin 21 duk suna kan wannan matsayin da suke ne ta hanyar maslaha. Babban abun da ya kamata jam’iyyar adawa ta kasance ta samu shi ne, samun hadin kai a tsakanin ‘ya’yata wanda hakan zai ba ta damar iya fuskanbtar kalubalen da ke gabansu, amma akasin haka za ta kasance cikin mawuyacin hali.
Watanni kadan bayan gudanar da zaben fid da gwani na shugaban kasa, jam’iyyar ta kara fadawa rikicin cikin gida na rarrabuwan kawuna tsakanin dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda har lamarin ya bijiro da batun tsige shugaban jam’iyyar na kasa, a matsayin hanya daya da zai zaunar da shi tare da magoya bayansa daga cikin jam’iyyar.
Idan har za a bijiro da batun tsige shugaban jam’iyya tun yanzu, wannan yana nuna cewa jam’iyyar tana iya samun nasarar cire dukkan masu rige da mukamai kafin wa’adin mulkinsu ya kare.
Magabatan shugabannin jam’iyyar PDP kamar irinsu Solomon Lar, Barnabas Gemade, Audu Ogbeh, Ahmadu Ali, Bincent Ogubulafor, Okwesilieze Nwodo, Bamanga Tukur, Ahmodu Sheriff da kuma Secondus, shugaban jam’iyyar PDP guda daya ne kacal ya samu nasarar kammala wa’adin mulkinsa shi ne Ali.
Tun daga lokacinsa har zuwa yau shekaru 24 da suka gabata babu wanda ya samu nasarar kammala wa’adin mulkinsa.
Tun daga lokacin da aka gudanar da zaben fid da gwani a cikin jam’iyyar, abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata, inda jam’iyyar ta mayar da hankali wajen sasanta Atiku da Wike, ganin yadda Wike ya fusata.
Wakazalika, ita ma jam’iyya mai mulki ta APC tana fuskantar kalubale a kan takarar Musulmi da Musulmi, lamarin da ya haddasa rarrabuwar kawuna da rashin bayayya ga shugaban jam’iyyar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Asiwaju Bola Tinubu, wanda yake kokarin girgiza kujerar shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
A cikin shekaru takwas, jam’iyyar APC ta yi shugabanni har guda biyar wadanda suka hada da Bisi Akande, John Oyegun, Adams Oshiomhole, Mai Buni da kuma Adamu.
A makon da ya gabata ne, alamu sun nana cewa gwamnonin jam’iyyar APC da wasu masu ruwa da tsaki suka zargi Adamu da rashin yin adalci tun lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar.
An dai zabi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC ne a watan Maris duk da irin babban adawar da yake da shi a wurin gwamnonin jam’iyyar.
Adamu dai ya samu goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen doke abokin takararsa Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa kuma a yanzu ya kasance sanata, wanda shi ne gwamnonin APC da manyan masu ruwa da tsaki suka mara wa baya.
APC tana ta kokarin dawo da lamara daidai tun bayan zaben fid da gwani na shugaban kasa, amma kuma a yanzu haka an samu sabuwar rarrabuwan kawuna a cikin jam’iyyar na tsige Adamu daga kan mukaminsa kafin gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa.
A bangaren jam’iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike sun kasance manyan masu jayayya a tsakani.
Wike wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, wanda ya samu rashin narasa daga wajen Atiku a watan Afrilu a zaben fid da gwani.
Ya bayyana cewa Atiku ya yi masa alkawarin zai ba shi gurbin takarar mataimakin shugaban kasa saboda kokarin da ya gudanar. Mafi yawancin manyan shugabannin jam’iyyar sun goyi bayan hakan ciki har da gwamnonin jam’iyyar.
Amma kwatsam sai Atiku ya bai wa Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa mataimakinsa, lamarin da ya haddasa rabuwan kai tsakaninsa da Wike.
A cewar Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, a cikin mambobin kwamitin PDP mai mutum 17, 14 daga ciki sun amince a bai wa Wike mataimakin shugaban kasa.
Ortom ya bayyana hakan ne a wata zantawa da gidan talabijin ta yi da shi, inda ya ce an zantar da shawarar cewa gwamnan Jihar Ribas ne mataimakin kafin lokacin da aka fitar da sunan Okowa.
Tun daga wannan lokacin ne Wike ya fara mu’amula da gwamnonin jam’iyyar APC da wasu masu ruwa da tsaki da ke cikin jam’iyyar, musamman wajen kaddamar da ayyukansa a Jihar Ribas.
A yanzu haka akwai kalubale a kan Ayu na ya sauka daga mukaminsa bisa yarjejeniyar cewa idan aka samu dan takarar shugaban kasa daga yankin arewa.
Magoya bayan Wike sun dage a kan sai Ayu ya sauka daga mukaminsa a matsayin matakin da zai goyi bayan Atiku a zaben shugaban kasa na 2023.
Sai dai kuma a cewar mai taimaka wa Ayu kan fannin yada labarai, Simon Imobo-Tswam, ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP, Iyiochia Ayu ba zai sauka daga kan mukaminsa ba, kuma babu wani shiri na ya sauka, domin an zabe shi ne na tsawan shekaru hudu.
Haka ma lamarin yake a bangaren APC na sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sauka daga kan mukaminsa. Jam’iyyar ta yi burus kan rahoton karaye-kiraye na cire Abdullahi Adamu daga mukaminsa.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Felid Morka ya bayyana cewa jam’iyyun adawa ne suke daukan nauyin rahotonnin da ke cewa dole sai shugaban ya sauka daga kan mukaminsa.
Adamu kamar dai Ayu wanda ya karya tsarin karba-karba na dan takarar shugaban kasa a PDP da ya fito daga arewa maimakon kudu, wanda mutanen yankin suke ganin su ne ya kamata su fitar da shugaban kasa, suna fuskantar kalubale a dukkan bangarorin jam’iyyun wanda ake ganin da wahala su kai babban zabe na watan Fabrairun 2023 a kan mukamansu.
Hakika jam’iyyun APC da PDP suna cikin hatsari wanda komi zai iya faruwa da dukkan jam’iyyun guda, wanda lokaci ne kadai zai iya tabbatar da hakan.