Rashin sa’ar cinikin Bayi a Arewacin Nijeriya hakan ya samu ne saboda wasu dalilai wadanda suka hada da, yadda shi mulkin mallaka bai goyi lamarin da yake da alaka da cinikin Bayi ba, ba domin komai ba sai saboda da akwai wadansu abubuwan da suke da nasaba da zamantakewa da kuma tattalin arziki a cikin sashen na Arewa, bugu da kari kuma ga lamarin nan na kyamar lamarin cinikin Bayi da su, kan su Turawan mulkin mallaka suke yi. Yayin da ainihin cinikin Bayin ana yin shi, kuma abin gaskiya ne ga mutane,yadda yake da kuma yadda ya shafi sauran yankuna, da rayuwar wuraren da ake yi yadda ta kasance.
Ga wasu daga cikin dalilan:
1.Mulkin mallaka ya shiga cikin lamarin:
Tsare-tsaren farko:
Da yake su Turawan mulkin mallaka su riga sun kasance sun zauna daram a Arewacin Nijeriya, daganan sai suka aiwatar da tsare tsarensu wadanda sun bullo da su ne domin hana cinikin Bayi.Suka maida lamarin wanda a shekarun baya ba matsala bace,amma yanzu a shar’ance, an hana shi,sannan kuma naka samu damar ‘yantar da wadanda Iyayen su suka zama Bayi bayan wani lokaci.
Yadda aka bullo ma lamarin:
Yayin da ake ta kokarin hana cinikin Bayi, su Turawan mulkin mallaka sun,amince da yadda cinikin Bayi ya shafi lamarin zamantakewa da tattalin arziki a sashen na Arewacin Nijeriya. Don haka sai suka bi abin sannu- sannu, har dai suka samu damar kawo karshen lamarin, ta hanyar bada zabi ga su Bayin su samu ‘yantar da kansu ta hanyar bada wani abu.
Matsalolin da aka fuskanta wajen tilasta hana cinikin Bayin:
Yadda Arewa take da yawa ga kuma fadi yana da matukar wuya a samu damar aiwatar da su tsare- tsaren,don haka sai ya kasance kamar ma an ce a ci gaba da cinikin Bayin,har zuwa wani lokaci.
2. Yadda ake zamantakewa da harkar tattalin arziki na abubuwan da suke a kasa:
Cinikin Bayi na cikin gida:
Arewacin Nijeriya ya dade tare da lamarin daya shafi bauta amma ta cikin gida,inda Bayi suke yin ayyuka daban – daban a gonaki,cikin gida, da kuma sauran lamurra masu kama da hakan.
Matsalar hana cinikin bayi a Arewa:
Lamarin cinikin Bayi an fara shi amma daga baya kuma aka bari, aka ci gaba da zamantakewa da yadda lamarin siyasa, yake, abinda yana da matukar wahala, ace cikin kankanen lokaci ace an samu matsalar tsayar da hakan.
Kin amincewa da a daina cinikin Bayai daga wurin wasu mutane:
Wasu mutane da wurare sun ki yarda da a daina yin cinikin Bayi, saboda su suna yi ma lamarin kallon kokari ne kawo masu wata matsala ce kan yadda suke tafiyra da rayuwarsu ta yau da kullun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp