• English
  • Business News
Thursday, September 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
2 months ago
in Nishadi
0
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin Rumbun Nishadi, yau kuma yana tafe ne da daya daga cikin jarumai masu tasowa a halin yanzu, wato Nusaiba Muhammad Ibrahim, wacce aka fi sani da Sailuba a cikin shirin Dadin Kowa, inda ta bayyana wa masu karatu irin nasarorin da ta samu game da harkar fim, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’ar tata ta fim.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu, Rabi’at Sidi Bala, kamar haka:

Ko za ki fada wa masu karatu cikakkenan sunanki da kuma sunan da aka fi sanin ki da shi?

Sunana Nusaiba Muhammad Ibrahim, amma an fi sanina da Sailuba Dadin Kowa.

 

Labarai Masu Nasaba

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

Masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinki?

An haife ni a garin Gombe, amma sai daga bisani na bar garin Gomben da zama na dawo Kano, tun ina ‘yar shekara biyar da haihuwa, sakamakon mahaifina yana aiki a Kanon. Kazalika, na girma a gaban iyayena, na yi firamare da sakandare duk a garin Kano, sannan kuma ban taba yin aure ba; budurwa ce ni.

 

Wace irin rawa kike takawa a cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood?

Ina fitowa ne a matsayin Jaruma kawai, amma kuma ina da niyyar zama mai bayar da umarni a nan gaba kadan insha Allah.

 

Me ya ja hankalinki, har kika tsunduma harkar fim?

Wato batu na gaskiya, fim yana burge ni kwarai da gaske, amma dalilin shigata sana’ar ita ce; wani fim aka yi sai wata arniyya ta musulunta, daga nan ne na ce; in dai har fim yana isar da sako, har ya zama silar gyaruwar al’umma, gaskiya zan zama daya daga cikin wadanda za su isar da wannan sako, tunda da ma raina yana so matuka gaya.

 

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?

Gaskiya ni ban sha wahala ba, dalili kuwa shi ne; dan fim ne ya sa ni a harkar ta fim, sannan kuma kamar yaya yake a wajena, dan Unguwarmu ne, iyayena da nasa sun zama kamar ‘yan’uwa.

 

Lokacin da kika fara sanar wa iyayenki cewa, kina son shiga harkar fim, wane kalubale da kika fuskanta daga wurinsu? 

Eh! Gaskiya na fuskanci kalubale, amma daga baya sun fahimce ni, sakamakon iyayen nawa masu fahimta ne.

 

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Ina ga zan samu kamar shekara takwas da farawa.

 

Ya farkon fara dora miki Kyamara ya kasance?

Ban ji tsoron komai ba, kuma Alhamdulillahi na samu yabo sosai daga wajen masu bayar da umarni da sauran abokan aiki.

 

Wane fim kika fara yi a farkon zuwanki?

Na fara ne da fim din Dadin Kowa.

 

Wace rawa kika taka a cikin shirin na Dadin Kowa?

Na fito ne matsayin Sailuba, inda na taka rawa a matsayin matar aure. Surukata ce ta auro wa mijina ni a kauye, saboda ba ta son matar dan nata da aura, sakamakon cewa; Beyerabiya ce, wato maman Rasaki kenan, ni kuma a nan na yi ta tsula tsiyata.

 

Bayan da aka fara haska fuskarki cikin shirin Dadin Kowa, ya kika ji a lokacin, sannan kuma yaya kika kasance da mutanen Unguwarku da sauran ‘yan’uwa?

Alhamdulillah! Wadanda suka san ni a gaske, sun biyo ni har gida suna kallona kamar a da ba su san ni ba, wadanda kuma ba su san ni ba, idan muka hadu abin ba dama, ga tarin alhairai daga masoya daga gurare daban-daban.

 

Bayan shirin Dadin Kowa da kika fito a ciki, ko akwai wasu fina-finan da kika fito ciki?

Eh, na yi wasu fina-finan da dama.

 

Kamar wadanne kenan?

Kamar irin su: Ni da Mijin Yayata, Matar Waye, Zaman Tare, Matar Kaddara da dai sauransu, dukkanninsu masu masu dogon zango ne kuma ni ce jarumar ciki.

 

Cikin wadannan fina-finai da kika zayyano, wane fim ne ya fi burge ki, kuma me yasa, sannan wace rawa kika taka a cikin shirin?

Ni da mijin Yayata, na fito ne a matsayin budurwa wacce take matukar son mijin yayarta.

 

Ya kika ji a lokacin da za ki taka rawa a wannan shirin?

Na ji dadi sosai, saboda zan yi abin da nake so; sannan kuma an kara min kwarin gwiwa, har muka yi muka gama babu wata matsala.

 

Ya batun masu kallo bayan shirin ya fita, ko kin samu wani kalubale daga gare su?

A a, kawai dai idan aka gan ni a zahiri, a kan yi mamaki tare da bayyana cewa; na fi kyau a fili, wasu ma har su ce ba su yi zaton cewa; ‘yar birni ba ce ni, sun yi zaton yadda nake ‘yar kauye a Dadin Kowa, a gaske ma haka nake.

 

A fina-finan da kika yi, wane fim ne ya fi haska ki; har mutane suke iya gane ki?

Dadin Kowa, sai kuma wannan fim din na Matar Waye, shi ma ba abin da zan ce gaskiya.

 

Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta, tun daga farkon zuwanki cikin masana’antar zuwa yanzu?

Gaskiya an samu, amma a da ne; yanzu cikin ikon Allah an samu daidaito.

 

Wadane irin nasarori kika samu game da fim?

Akwai nasarori da dama kamar ta fuskar samun kudi, mota, kayan sakawa, turaruka da sauran makamantansu.

 

Ko kina da ubangida a masana’antar Kannywood?

Kwarai da gaske ina da su, akwai Adam Musa Adam da kuma Usman Adam Hali Dubu.

 

Kafin ki fara fim, wadane jarumai ne suka fi burge ki har kike jin dama ki zama tamkar su?

Ina kowace jaruma, domin kuwa dukkaninsu suna burge ni.

 

Yaushe kike sa ran yin aure?

Duk lokacin da Allah ya kawo shi, a shirye nake.

 

Ko akwai wanda ya taba cewa yana son ki zai aure ki a masana’antar?

Kwarai da gaske, akwai.

 

Ko za mu iya jin sunansa?

A’a gaskiya.

 

Mene ne ra’ayinki game da auren dan fim?

Zan iya aurensa mana, ai babu wata matsala a ciki.

 

Wane irin namiji kike so ki aura?

Ya kasance Musulmi, mai ilimi, wanda kuma yake da cikakkiyar sana’a.

 

Wace shawara za ki bai wa abokan aikinki na masana’antar Kannywood?

Da farko dai, ya kamata mu hada kanmu, sannan mu kiyaye abin da zai bata sunan sana’ar tamu, mu kuma yi kokari wajen kare mutuncinmu, wannan shi ne a takaice.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa wannan masana’anta?

Su tabbata sun shigo da niyya mai kyau, sannan kuma su yarda cewa; sana’a suka zo yi, ba wani abu daban ba.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina fatan alhairi ga kowa da kowa, musamman masoyana.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Next Post

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Related

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)
Nishadi

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

4 days ago
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
Nishadi

Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba

2 weeks ago
Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
Nishadi

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

3 weeks ago
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

4 weeks ago
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
Nishadi

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

1 month ago
Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
Nishadi

Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

1 month ago
Next Post
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

LABARAI MASU NASABA

Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

September 11, 2025
Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

September 11, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

September 11, 2025
Najeriya: Ajandar Jagorantar Duniya Ta Ba Da Gudummawa Ga Tsarin Kasashen Duniya

Najeriya: Ajandar Jagorantar Duniya Ta Ba Da Gudummawa Ga Tsarin Kasashen Duniya

September 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 10 A Jihar Neja

September 11, 2025
DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

September 11, 2025
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi

‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata

September 11, 2025
Ganawata Da Macron Ta Yi Amfani – Tinubu

Ganawata Da Macron Ta Yi Amfani – Tinubu

September 11, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya

September 11, 2025
Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL

Mele Kyari Ya Bayyana A Ofishin EFCC Kan Zargin Badaƙalar Dala Biliyan 7.2

September 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.