Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bincike na musamman domin gano gaskiyar lamarin da ya sa Kwamishinan Sufuri na jihar, Hon. Ibrahim Ali Namadi, ya karɓi belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi a Kano, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a madadin Gwamnan. An bai wa kwamitin wa’adin mako guda domin gudanar da bincike da kuma gabatar da rahoton da ya dace.
- Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano
- Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano
Kwamitin na mutane takwas zai kasance ƙarƙashin jagorancin Mai ba Gwamna shawara kan harkokin shari’a da kundin tsarin mulki, Barrister Aminu Hussaini. Mambobin kwamitin sun haɗa da: Barr. Hamza Haladu, Barr. Hamza Nuhu Dantani, Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Muhammad Sani (rtd), Comrade Kabiru Dakata, da Farfesa Mamun Mustapha daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.
Sauran mambobin sune: Alh. Abdullahi Mahmud Umar daga Hukumar Kula da Ma’aikata, da kuma Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Gudanarwa da Ayyuka na Gwamnati (SSG), wadda za ta kasance sakatariyar kwamitin.
Barrister Aminu Hussaini, a madadin sauran mambobi, ya gode wa gwamnatin Kano bisa gaggauta ɗaukar mataki, tare da tabbatar da cewa za su gudanar da aikin cikin gaskiya, da kwarewa, da riƙon amana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp