Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya daina dogaro da rahotannin gwamnoni kawai dangane da halin tsaro da ake ciki a Nijeriya.
Jam’iyyar ta ce ya kamata ya fita ya ganewa idonsa ya kuma saurari halin da talakawa ke ciki.
- Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
- Rikicin Makiyaya Da Manoma: An Kashe Mutum Daya, Gidaje 31 Sun Kone A Abuja
Wannan martani ya biyo bayan jawabin mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Daniel Bwala, wanda ya bayyana cewa matsalar tsaro ta ragu tun bayan da Tinubu ya hau mulki.
Bwala, ya ce an samu raguwar kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihohin Benuwe, Filato da yankin Kudu Maso Gabas.
Amma mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya musanta hakan.
Ya ce har yanzu matsalar tsaro tana addabar sassan Nijeriya da dama, kuma ana yaudarar shugaban ƙasa game da hakan.
Ya ce, “Idan Shugaba Tinubu yana sauraron labarai masu daɗi kawai daga waɗanda ke son faranta masa rai, to yana rayuwa ne a cikin duhu.”
Abdullahi ya bayyana cewa al’umma da dama a Nijeriya har yanzu na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, kuma mutane na rayuwa cikin tsoro da fargaba.
Ya ce ba daidai ba ne a riƙa nuna kamar abubuwa sun inganta, alhalin jama’a na cikin hali na ƙunci ba.
Jam’iyyar ADC ta kuma soki gwamnatin Tinubu da cewa ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sun ce maimakon fadar shugaban ƙasa ta riƙa kare shugaban da labaran da ba su dace ba, kamata ya yi su mayar da hankali kan nemo hanyoyin da za su kawo zaman lafiya da tsaro ga ‘yan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp