Kamar yadda bayanai suka nuna, tun fil azal, tsibirin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Kuma Sinawa ne suka fara gano yankin Taiwan. Haka kuma, akwai bayanai game da yankin Taiwan a cikin littattafan tarihi na kasar Sin wadanda aka rubuta yau shekaru 1700 da suka gabata. Tun zamanin daular Yuan ta kasar Sin wato tsakanin shekarar 1206 zuwa shekarar 1368, gwamnatin kasar Sin ta fara kafa hukumomi a yankin Taiwan, domin tafiyar da harkokin yanki yadda ya kamata.
A shekarar 1894, kasar Japan ta kaddamar da yakin da bai cancanta ba a kasar Sin, bayan rashin nasarar gwamnatin kasar Sin na lokacin a wannan yaki, sai kasar Japan ta mamaye yankin Taiwan na kasar Sin.
Daga bisani kuma, kasar Japan ta sanar da mika wuya a yakin duniya na biyu a shekarar 1945, inda ta nuna amincewa da sanarwar Potsdam da sanarwar Alkahira ba tare da wani sharadi ba, wannan ya sa, ta mayar da yankin Taiwan ga kasar Sin. Daga shekarar ce kuma, kasar Sin ta samu cikakken ikon kan yankin Taiwan.
A ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949 ne, aka sanar da kafa Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin a hukumance, sa’an nan, wasu sojojin adawa na jami’yyar Kuomintang suka arce zuwa yankin Taiwan, biyo bayan rashin nasara a yakin basasar da suka gwabza tsakaninsu da dakarun JKS. Daga bisani kuma, suka mamaye yankin Taiwan bisa goyon bayan da suka samu daga gwamnatin kasar Amurka.
Wannan ya sa, batun Taiwan ya kasance batun da ba a warware ba har yanzu sakamakon yakin basasar Sin. Kasancewar babban yanki da na Taiwan na kasar Sin daya ne bai taba canzawa ba kuma ba za a iya canza shi ba.
Haka kuma babu wanda zai kalubalanci ka’idar kasar Sin daya tak a duniya. Amincewa da wannan manufa, ita ce tushen kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da sauran kasashe, kuma kasar Sin ba za ta taba yarda wani ya kalubalanci wannan manufa ba.
Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma yankin Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin wanda ba za a iya taba raba shi daga kasar Sin ba. Kuma, gwamnatin Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar Sin bisa doka. Wannan shi ne muhimmin bayani game da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, wanda ya samu amincewar gamayyar kasa da kasa.
A shekarar 1943, shugabannin kasashen Sin da Amurka da Burtaniya sun bayar da “Sanarwar Alkahira” a kasar Masar, wadda ta bayyana karara cewa, dukkan yankunan da kasar Japan ta sace daga kasar Sin, ciki har da Taiwan, a cikin yakin da aka yi tsakanin Sin da Japan a karshen karnin 19, dole ne ta maido su ga kasar Sin.
Sannan ita ma yarjejeniyar Potsdam ta shekarar 1945 ta tabbatar da cewa, wajibi ne a aiwatar da sharuddan dake kunshe cikin sanarwar Alkahira.
A watan Oktoba na shekarar 1971, an zartas da kuduri mai lamba 2758 yayin babban taron MDD karo na 26, inda aka bayyana cewa, Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin ta zama wakiliyar kasar Sin daya tilo a MDD bisa dokoki.
Bugu da kari, a lokacin da Sin da Amurka suka kulla huldar jakadanci a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1979, sassan biyu sun amince cikin wasu sanarwoyin hadin gwiwa cewa, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ce halastacciyar gwamnatin Sin, yankin Taiwan wani bangare ne na jamhuriyar jama’ar Sin, ba a iya balle shi daga kasar Sin ba, kasar Amurka ta mutunta cikakken yankin kasar Sin da ikonta na mulkin kasar.
Duk da wadannan shaidu da bayanai na tarihi, a kwanakin baya, shugabar majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kau da kai ta gudanar da wannan haramtacciyar ziyara, domin neman cimma wani buri na siyasa da neman tayar da zaune tsaye da keta ka’idar kasar Sin daya tak a duniya, da ma dokoki na kasa da kasa. Lamarin da ya gamu da yin Allah wadai daga bangarori da dama a ciki da wajen kasar Sin.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jaddada matsayin kasar Sin da batun yankin Taiwan kan wannan ziyara, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan kammala taron ministocin wajen kungiyar ASEAN. Har kullum kasar Sin tana nacewa ga kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma yankin Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba.
Wang ya ce, kasar Amurka ta yi kuskure a bangarori uku, dangane da ziyarar gangancin da shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, a matsayin mayar da martani ga yanayin da ake ciki na baya-bayan nan da yadda bangaren Amurka yake jujjuya maganar.
Da farko, bangaren Amurka ya yi katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin. Kuma duk da sanarwa da kuma gargadin da kasar Sin ta sha yi, amma Amurka ta yi gaban kanta, ta kuma shirya wa jami’a mai matsayi na uku a gwamnatin Amurka don kai wannan ziyara zuwa yankin Taiwan na kasar Sin.
Na biyu, Amurka ta hada kai tare da goyon bayan masu neman “’yancin kan Taiwan”, don haka, wajibi ne kowace kasa ta kiyaye hadin kan kasa, kuma bai kamata ta taba bari ‘yan aware su rika nuna halin ko-in-kula ba.
Na uku, da gangan Pelosi ta yi wa zaman lafiya zagon kasa a mashigin tekun Taiwan. Kuma kamar yadda kowa ya sani, a ko da yaushe, Amurka ce take fara haifar da matsala, sannan kuma ta yi amfani da ita wajen cimma manufofinta bisa dabarun da ta tsara.
Wang ya ce, kasar Sin ta yaba da fahimtar juna da goyon bayan da kasashe daban-daban suka nuna mata. Yana mai cewa, yayin da ake gudanar da ayyukan cin zarafi na kashin kai daga lokaci zuwa lokaci, ya kamata kasashen duniya su cimma matsaya karara, da yin magana da babbar murya, ta yadda za su kiyaye muhimman ka’idojin dangantakar kasa da kasa, da dokokin kasa da kasa, da kiyaye ’yanci da muradun dukkan kasashe masu tasowa.
Domin sake jaddada matsayinta game da yankin na Taiwan, bayan haramtaciyar ziyarar, kasar Sin ta sanar da soke wasu shirye-shirye da aka tsara gudanarwa tsakanin Sin da Amurka da haramta shigo da wasu nau’in kayayyakin daga yankin Taiwan zuwa babban yankin kasar Sin, da kadamar da atisayen hadin gwiwa da rundunar sojojin ‘yan tarda jama’ar kasar Sin(PLA) ta yi a rawayen kogi da tekun Bohai da wasu sassa na kewayen yankin Taiwan, a wani mataki na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Cikin matakan da Sin ta dauka, sun hada da soke shirin da aka yi ta wayar tarho tsakanin kwamandojin rundunonin sojin kasashen Amurka da Sin da kuma ganawar da za a yi tsakanin ma’aikatunsu na tsaro, tare da sauran wasu matakai.
Haka zalika, kasar Sin ta yanke shawarar kakabawa Pelosi tare da iyalanta takunkuman da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Wannan matakin martani ne da Sin ta dauka, saboda nacewar da kakakin majalisar wakilan Amurka ta yi, na kai ziyara yankin Taiwan, duk da adawa da korafin da kasar Sin ta gabatar.
Atisayen da rundunar sojojin PLA dake gabashi ta gudanar da ba da horo na hadin gwiwa a kewayen ruwa da sararin samaniyar tsibirin Taiwan, duk sun gudana kamar yadda aka tsara.
Wadannan atisayen sun fi mayar da hankali ne kan ayyukan hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa da hare-haren da ake kaiwa a kan teku. Rundunar sojin ruwa ta tura da dama daga cikin jiragen ruwa, da jiragen yaki, da jiragen harba makamai masu linzami, a wani aikin hadin gwiwa na jiragen ruwan yaki dake karkashin teku.
Jiragen sintirin yaki dake karkashin teku, da jiragen ruwa na yaki, da jirage masu saukar ungulu, sun yi hadin gwiwa wajen atisayen. Wadannan sun hada da binciken karkashin ruwa, da hare-haren gano abokan gaba, da ayyukan tsaro. Daga karshe an kammala wadannan atisaye cikin nasara.
Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Ma Xiaoguang ya gargadi Cai Yingwen da jam’iyyar DPP dake jagorancin yankin Taiwan da suyi hattara game da yunkurinsu na neman ballewar yankin,yana mai cewa, kuskuren da suka yi zai kara saurin dakile su, da tsunduma Taiwan cikin mawuyacin hali.
Har wa yau, Ma Xiaoguang ya ce, babban yankin kasar Sin ya yanke shawarar daukar matakan hukunta jagororin ’yan aware na Taiwan masu taurin kai, wadanda suke fakewa da sunan “dimokuradiyya” da “hadin gwiwar neman ci gaba” wajen gudanar da aikace-aikacen neman ballewar yankin daga kasar Sin.
Yanzu haka kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da dinkuwar kasar Sin a sabon zamani”, inda aka bayyana cewa, kamata ya yi a bar jama’ar kasar Sin su yanke shawara kan al’amuran kasarsu. Wannan na nufin, batun Taiwan, harkokin gidan kasar Sin ne, wanda ya shafi babbar moriyar kasar, da kaunar da Sinawa suke nuna wa kasarsu, don haka, ba su yarda kuma ba zasu taba yarda da tsoma baki daga kasashen ketare kan dukkaan harkokin da suka shafi cikin gidan kasarsu ba.
Kafin fitar da wannan takardar bayanin, ziyarar da shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Pelosi, ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, ba tare da amincewar gwamnatin Sin ba, ya lalata yanayin tsaron zirin Taiwan, da tsananta rikici tsakanin Amurka da Sin.
Wannan ne ma ya sa, kasar Sin ta sanar da fitar da wannan takardar bayani, don mayar da martani ga wannan ziyarar ta neman tsokana da keta hurumin kasar Sin, tare da yin cikakken bayani kan dabarun kasar Sin dangane da yadda za a daidaita batun Taiwan a sabon zamani, da yadda hakan zai taimaka a kokarin tabbatar da zaman lafiya da walwala a yankin Asiya da tekun Pesific, gami da sauran sassa na duniya.
A karon farko, takarda bisa tsari ta bayyana fatan sake hadewar bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, a karkashin tsarin “kasa daya, tsarin mulki iri biyu”. Wanda ya nuna irin babban ci gaban da yankin Taiwan zai iya samu, da ba da tabbaci ga moriyar mutanen yankin Taiwan, da samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific, da ma sauran sassan duniya, da makamantansu.
A karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Sinawa da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.4 suna son ganin dinkuwar kasarsu cikin lumana. Haka kuma ba za su taba hakura da yunkurin ‘yan aware na neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin ba. Sinawa suna da niyya mai karfi ta fuskar kare mulkin kai da cikakkun yankunan kasarsu, kana suna da hakima, da jajircewa da ake bukata, wajen tabbatar da dinkuwar kasar Sin a nan gaba
Yunkurin Amurka na neman dakile kasar Sin ta hanyar fakewa da batun yankin Taiwan,wanda masana ke cewa, tamkar wasa da wuta ne, ba zai taba yin nasara ba, kuma ba zai iya canza yanayin tarihi dake tabbatar da cewa, babu makawa wata rana, yankin Taiwan zai dawo karkashin ikon kasar Sin, tare da zaburar da al’ummar Sinawa da su hada kai, tare da gaggauta gina babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani mai sigar kasar Sin.
Kuma cimma burin dinkuwar kasar Sin cikin lumana, ba wai babbar nasara ce kadai ga Sinawa ba, babbar nasara ce ga daukacin al’ummomin kasashen duniya. Mai hakuri aka ce ya kan dafa dutse har ma ya sha romonsa. (Ibrahim Yaya)