A kusan ƙarni biyu da suka gabata, wasu ƙwararru da masana a fannin aikin noman ƙasar nan, sun danganta ɗimbin dalilan da suka sanya ake yawan samun hauhawar farashin tumatir a kasuwancinsa da ake yi a wannan ƙasa, wanda hakan ke shafar manoman da ke noma shi da kuma masu sayen sa, domin amfanin yau da kullum.
Kashi 65 na tumatirin da ake kai wa ƙasashen Afirka ta Yamma, daga Nijeriya ake fitar da shi duba da cewa; Nijeriya ce ƙasa ta biyu a Afirka da ke noman sa, wadda kuma ta kasance ta 14 a duniya, wajen noman shi.
Sai dai, Babban Shugaban Cibiyar Bincike ta NIHORT, dakta Ephraim Nwanguma ya bayyana cewa; duk shekara, Nijeriya na shigo da kimanin tan 150,000 na tumatir daga ƙasashen ƙetare, wanda kuɗinsa ya kai kimanin dala miliyan 170 duk da cewa; ƙasar na iya yin nomansa da yawa.
- Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
- Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
Ya ƙara da cewa, Nijeriya ce ta uku a Afirka wajen shigo da tumatirin gwangwani Afirka, inda ta kai mataki na 13 a duniya wajen shigo da shi cikin ƙasar.
Kazalika, sashen kula da samar da abinci na Majalisar ɗinkin ɗuniya (FAO), ya danganta wadannsn ƙalubale a kan asarar da manomansa suke yi, mussaman a farkon girbe shi, wacce take kai wa ta kusan kashi 50, inda suke samun kashi 20 kacal, na wadanda suka noma.
A bisa ƙiyasin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya yi, ya ce; tumatirin da ake nomawa a shekara a Nijeriya, ya kai kimanin tan miliyan 1.701, wanda kuma ake amfani da shi a shekara ya kai aƙalla tan 2.93, inda wannan adadin ya nuna cewa; a shekara, ana samun ƙarancinsa da ya kai na kimanin tan miiyan miliyan 1.2, inda kuma a duk shekara ake cike giɓin da ake da shi na wanda ake shigo da shi kimanin na ƙalla dala biliyan 2.5.
Wani ƙiyasi da kamfanin ‘Reportlinker’ ya gudanar ya ce, buƙatar tumatir a shekara , za ta ƙaru zuwa tan miliyan 3.01 a 2028.
Jerin Manyan ƙalubalen da Ke Shafar Farashin Tumatir A Nijeriya:
1- Noman Tumatir daga Kaka Zuwa Kaka:
Hakan na haifar da tsadar farashinsa da kuma ƙarancinsa, musamman duba da cewa; nomansa a Arewacin Nijeriya, na faraway ne daga watan Nuwamba zuwa watan Maris, inda hakan ya sa ba a yin noman na gajeren zango, wanda kuma farashinsa ke raguwa a daidai lokacin.
Amma a lokacin damina, farashinsa na ƙaruwa ne sakamakon yadda yake yin ƙaranci.
2- Cututtukan da Ke Lalata Tumatirin da Aka Shuka:
ɓarkewar cututtuka, kamar irin su Tuta da ke lalata tumatirin da aka shuka, na shafar tashin farashinsa da kuma ƙarancinsa a Nijeriya.
3- Rashin Kayan Adana Tumatirin da Aka Noma:
Wannan na haifar wa da manomansa yin asara bayan sun girbe shi, inda aka ƙiyasta kashi 40 cikin 100 na Tumatirin da aka girbe, ba ya kai wa ga masu sayensa kai tsaye, musamman ganin cewa; tuni ya riga ya lalace.
4- Rashin Samun Bayanai daga Kasuwanni:
Wannan ƙalubale na haifar wa da manomansa asara mai yawan gaske, saboda rasahin samun bayanai daga kasuwanni kafin su kai ga shi kasuwa, domin sayarwa.
5- ƙarancin Kayan Nomans Tumatir Na Zamani:
Hakan na sanya manoman tumatiri gazawar samun amfani mai yawa tare da yin asara bayan sun girbe shi.
6- Faɗuwar darajar Naira da ƙarancin ƴan ƙwadagon da Ake dauka Haya:
Akasarin ƴan ƙwadagon da ake dauka haya daga ƙasashen da ke maƙwabtaka da Nijeriya, don yin aiki a gonakin da aka shuka tumatir a Kudacin ƙasar, saboda faɗuwar darajar Naira, suna komawa ƙasashensu ne.
7- Rashin Samar da Tsare-Tsare Masu ɗorewa Ga Fannin:
Babban bankin ƙasa (CBN) a 2013, ya gudanar da taruka iri daban-daban tare da samar da tsare-tsare masu ɗimbin yawa ga wannan fanni, bisa hadaka da Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara da Ma’aikatar Masana’antu da Zuba Hannun Jari, domin daidaita fannin na noman tumatir a faɗin wannan ƙasa, amma duk da haka, haƙan bai kai ga cimma ruwa ba.
Kazalika, a 2022 zuwa 2026, gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro da tsari na ƙasa a kan noman wannan tumatir, musamman domin a rage asarar da manoma ke tabkawa, bayan girbi da kuma rage yawan shigo da shi daga ƙasashen ƙetare.
Sai dai, rashin wanzar da tsarin, ya sa lamarin ya koma tamkar ƴar gidan jiya.
8- Tsadar Kayan Noman Tumatir:
Kayan noman tumatir, musamman takin zamani da Iri, na da matuƙar tsada a Nijeriya, wanda idan manomansa suka shuka shi tare kuma girbe shi, ba sa iya samun wata ribar a zo a gani, inda hakan ke sanya farashinsa ya riƙa ƙaruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp