Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina ta sanar da kama mutane 302 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, da kuma ceto sama da mutane 50 da aka sace a cikin watan Yulin 2025.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ya wakilci Kwamishinan ‘Yansanda, CP Bello Shehu, a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’a, ya gode wa Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bisa goyon baya da ya bayar wanda ya taimaka matuƙa wajen yaƙi da laifuka a jihar.
Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama akwai:
- Mutum 14 da ake zargi da fashi da makami
- Mutum 22 da ake zargi da kisa
- Mutum 25 da ake zargi da aikata fyaɗe
- Mutum 20 da ake zargi da lalata kayan gwamnati
- Mutum 8 da ake zargi da damfara
- Mutum 26 da ake zargi da sayar da miyagun ƙwayoyi
- Mutane 194 da ake zargi da sauran laifuka daban-daban
DSP Aliyu ya ƙara da cewa rundunar ta daƙile hare-haren ‘yan fashi da dama a tsawon lokacin.
Kayan da aka ƙwato sun haɗa da:
- Dabbobi 199 da aka sace (shanu 161 da tumaki 68)
- Motoci guda 3 da aka sace
- Babura 2 da ake zargi an sace su
- Miyagun ƙwayoyi da yawa ciki har da tabar wiwi
- Wayoyin wutar lantarki da aka lalata
DSP Aliyu ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar saboda haɗin kai da suka bayar, yana mai cewa ba za a cimma nasarorin ba tare da taimakon jama’a ba.
Ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa ‘yansanda goyon baya, tare da kai rahoton duk wani abun zargi ta waɗannan layukan gaggawa: 0815697777722, 0902220969033, da 07072722539.
“Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina za ta ci gaba da ƙoƙarinta don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp