Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku.
Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019.
- Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfaɗo Da Noman Dabino – Shettima
A cikin shekaru 27 na aikinsa, Farfesa Adamu ya yi fice a koyarwa, da bincike, da gudanarwa a fannin ilimi. Ya taɓa aiki a matsayin likitan dabbobi na hukumar Youth Corps, sannan ya samu damar koyarwa a Jami’ar Noma ta Makurdi inda ya kai matsayi na Farfesa. Haka kuma ya rike muƙamai da dama ciki har da Mataimakin Tsangaya na Kwalejin Likitocin Dabbobi.
Sanarwar ta bayyana cewa sabon VC zai tallafa wa Kwamitin Gudanarwa don kammala zaɓin cikakken Mataimakin Shugaban Jami’a bisa ga ƙa’idojin doka, kuma an gode wa Farfesa Lar kan jajircewarta a lokacin da ta riƙe mukamin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp