Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Brazil wajen zama misali na hadin kai da dogaro da kai tsakanin manyan kasashen dake cikin kasashe masu tasowa da gina duniya mai adalci da dorewa.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yau Talata, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.
- Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Sun Yi Bikin Murnar Karɓar Kyautar N23m Daga Bankin STANBIC IBTC
Da yake bayyana kungiyar BRICS a matsayin muhimmin dandalin cimma matsaya tsakanin kasashen masu tasowa, Xi Jinping ya taya Brazil murnar nasarar da ta cimma na karbar bakuncin taron BRICS na baya bayan nan.
Shugaban na Sin ya kuma yi kira ga kasashe masu tasowa su kare tsarin adalci da daidaito a duniya, da ka’idojin dangantakar kasa da kasa tare da kare halaltattun hakkoki da muradun kasashe masu tasowa.
Ya ce ya kamata Sin da Brazil su ci gaba da hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya da tabbatar da nasarar babban taron MDD kan sauyin yanayi dake tafe a birnin Belem na Brazil, da karfafa rawar da rukunin kasashen nan masu rajin shawo kan batun Ukraine suke takawa wajen inganta warware matsalar a siyasance. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp