Rundunar ’Yansandan Jihar Gombe ta kama wani hakimi mai shekara 55 daga garin Zambuk, a Ƙaramar Hukumar Yamaltu/Deba, kan zargin yi wa wata yarinya mai shekara 12 fyaɗe.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kai rahoton lamarin ofishin ’yansanda na Zambuk a ranar Asabar.
- ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
- Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
’Yansanda sun je wajen da abin ya faru, suka kai yarinyar asibitin Janar na Zambuk domin duba lafiyarta, sannan suka kama wanda ake zargin.
A wani labarin daban, ’yansanda a Bajoga, Karamar Hukumar Funakaye, sun gano igiyoyin wutar lantarki, bututun ƙarfe, da ƙusoshin layin dogo da aka sace.
Haka kuma, an kama wani yaro mai shekara 18 da ake nema kan laifin fashi da makami a Kwadom, Yamaltu/Deba.
An ce ya amsa cewa an aikata fashi da makami sau biyu da shi, kuma yanzu hakan ana shari’arsu a kotun jihar Gombe.
An miƙa shi tare da kayan da aka gano ga Sashen Yaƙi da Tashin Hankali domin ƙara gudanar da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp