Kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da gudunmuwa ga hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ta MDD (UNRWA), tare da kira ga kasa da kasa da su ci gaba da tallafawa hukumar wadda ta ce tana fama da matsaloli saboda yakin da ake yi a Gaza da kuma wagegen gibin kudi.
Shugaban ofishin kula da harkokin Palasdinu na kasar Sin Zeng Jixin da Karim Amer, daraktan sashen kula da hadin gwiwa na UNRWA ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da gudumuwar, jiya Laraba a Amman, babban birnin kasar Jordan. Yarjejeniyar wani bangare ne na gudunmuwar da Sin ke ba hukumar a kowacce shekara.
Zeng Jixin ya yaba wa UNRWA bisa rawa mai matukar muhimmanci da take takawa wajen bayar da agajin jin kai ga miliyoyin ‘yan gudun hijirar Palasdinu. Ya ce bayan barkewar rikici a Gaza, Sin ta kara yawan gudunmuwarta na shekara, tare da samar da kayayyakin kiwon lafiya da sauran kayayyakin agaji.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp