Mamban kwamitin raya kasa da yin gyare gyare na kasar Sin Liu Liehong, ya ce yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar na 14, kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare kan amfani da bayanan bunkasa harkokin kasuwa, tare da hanzarta aiwatar da sauye-sauyen bunkasa fasahar zamani da kiyaye muhalli, don samun sakamako mai ban mamaki.
Liu Liehong wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da kididdiga ta kasar, ya bayyana haka ne yau Alhamis a gun taron manema labarai mai taken “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar na 14 cikin inganci”, wanda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar.
A cewarsa, a lokacin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar na 14, manyan ababen more rayuwa na zamani na kasar sun samu ci gaba mai yawa, wanda yake kan gaba a duniya a fannoni da dama. Ya kara da cewa, zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2025, jimillar tashoshin 5G ya kai miliyan 4.55, adadin masu amfani da manyan hanyoyin sadarwa na gigabit ya kai miliyan 226, kuma karfin na’ura mai kwakwalwa ya kai matsayi na biyu a duniya, wanda ya haifar da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa yadda ya kamata. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp