Amfani da gishiri a cikin abinci ko abin sha fiye da kima, na iya haifar ko sanadiyyar kamuwa da cutar hawan jini. Sannan kuma, hawan jini na da hadarin haifar da cutukan zuciya da kuma jijiyoyin jini.
Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Gidauniyar Zuciya ta Birtaniya, sun kayyade yawan gishirin da ya kamata mutum ya yi amfani da shi a rana cewa, ya zamanto kasa da ma’aunin giram shida, wato kwatankwacin mitsitsin cokalin shayi guda kenan kacal.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”
Sai dai kuma, an lura cewa; kashi uku cikin hudu (3/4) na yawan gishirin da ake amfani das hi ko ci, ba a ma sanin cewa; an ci wannan adadin. Domin kuwa, ana zuba gishirin ne tun lokacin da ake sarrafa abinci ko abin sha, saboda haka; abu ne mai matukar wahala a iya gane yawan gishirin da ka ci a kowace rana.
Har ila yau, abubuwan da ke makare da gishiri sun hada da; nau’o’in magi, musamman farin magi, burodi, biskit, kek, yagwat, lemukan gwangwani da na roba, sarrafaffen abinci da ke zuwa a leda, gwangwani ko roba da dai sauran makamantansu.
Domin kaurace wa cin wannan gishiri fiye da kima, ana iya amfani da barkono ko sauran jinsinsa, kayan kamshi, ciyayi, ganyayyaki, tafarnuwa, albasa, ruwan lemon fata da dai sauransu, domin samar da dandanon abincin da ake bukata, maimakon amfani da gishiri ko magi.
Haka zalika, kayyade ko karanta cin gishiri zuwa kasa da giram shida a kullum, ko shakka babu zai rage hadarin kamuwa da:
– Hawan jini
– Bugun zuciya
– Shanyewar barin jiki
– Kassarewar zuciya da sauran matsalolin zuciya da jijiyoyin jini.














