Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga Jami’ar Sojin Nijeriya da ke garin Biu (NAUB), domin bunƙasa bincike da kuma ci gaban gine-gine a jami’ar.
Zulum ya sanar da hakan ne a fadar gwamnati da ke Maiduguri yayin da ya karɓi babban jami’in jami’ar, Farfesa Lawan Bala Buratai tare da wasu manyan jami’ai na makarantar. Gwamnan ya yabawa ƙoƙarin samar da dokokin da za su tabbatar da ɗorewar jami’ar a nan gaba.
- Gwamna Bala Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Gwamnan Bauchi A Zamanin Mulkin Soja
- Fim Na Kisan Kiyashin Da Sojojin Japan Suka Yi A Birnin Nanjing Na Samun Karbuwa A Kasar Sin
Bugu da ƙari, Zulum ya sanar da bayar da guraben karatu ga dalibai marasa galihu daga dukkan ƙananan hukumomin jihar 27 domin su samu damar karatu a jami’ar. Ya ce an umarci kwamishinan ilimi da ya duba yawan ɗaliban da jami’ar za ta iya karɓa domin a tallafa musu.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin tallafa wa kafa kwalejin kimiyyar lafiya a NAUB domin ƙara yawan likitoci da ma’aikatan lafiya a jihar. A nasa jawabin, shugabancin jami’ar ƙarƙashin Farfesa Buratai ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, tare da neman ƙarin guraben karatu musamman a ɓangaren injiniya da fasaha.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp