Yayin da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ke ziyara a kasar India, kasashen Sin da Indian sun amince da ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakaninsu.
A cewar Wang Yi, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa da jimilar al’ummarsu ta kai sama da biliyan 2.8, ya kamata kasashen biyu su zama misali ga kasashe masu tasowa wajen kara karfi ta hanyar hadin kai da bayar da gudunmawa ga cudanyar kasashe da rarrabuwar iko tsakanin kasa da kasa, maimakon kasancewa karkashin ikon wata kasa ko wasu ’yan tsirarun kasashe.
Tabbas tattaunawar da ake yi da tuntubar juna tsakanin India da Sin, abun yabawa ne saboda ya nuna wa duniya cewa, ba duka aka taru aka zama daya ba. Kuma manuniya ce cewa, akwai hanya mai bullewa ta samun zaman lafiya da kyautatuwar dangantaka ta hanyar tattaunawa, maimakon fin karfi da fito na fito.
Ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu, tuni aka fara aiwatar da matsayar da shugabanninsu suka cimma tare da farfado da harkokin musaya da tattaunawa a tsakaninsu a dukkan matakai. Har ministan harkokin wajen India ya godewa kasar Sin bisa yadda ta saukakawa Indiyawa masu ziyarar ibada a yankin tsaunika da ma tabkunan lardin Xizang na kasar Sin. Wadannan sun nuna kyakkyawar niyyar kasashen biyu ta daidaita dadaddiyar huldar dake tsakaninsu.
Yayin da har yanzu wasu kasashe suka kasa hakura da tsohon ra’ayinsu na danniya da fin karfi, kasar Sin ta zama jagora mai haskawa kasashe masu tasowa wata hanya ta daban ta zaman lumana da samun ci gaba ba tare da nuna fin karfi ba. Haka kuma, ta kasance mai riko da hannayensu da kasancewa abun dogaro.
Dawowar kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Indiya, zai taimaka gaya wajen tabbatar da zaman lafiya a shiyyarsu. Kasancewarsu manyan abokan cinikayya kuma manyan kasashe masu tasowa haka ma kasashe mafiya yawan al’umma a duniya, ba su kadai da shiyyarsu ne za su amfana da kyautatuwar dangatakar ba, za ta bada gaggarumar gudunmawa ga ci gaban duniya ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da zaman lafiya, tare da zama misalin zaman jituwa bisa aminci da hadin gwiwa a tsakanin makwabta. Tabbas ina da yakinin na gaba kadan, bisa namijin kokarin da Sin ke ci gaba da yi na kokarin samar da sulhu da zaman lafiya a siyasance, za a kai ga kawar da danniya da babakere da cin zali a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp