Jam’iyyar NNPP na shirin yanke wasu muhimman kudirori a taron majalisar zartarwarta na kasa (NEC) da za ta yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025, a Abuja.
Alamu dai na nuni da cewa, a wajen taron, jami’iyyar za ta yanke mafita kan makomarta a babban zaben shekarar 2027.
- Kasar Sin Ta Zama Jagora Mai Haskawa Duniya Sabuwar Hanyar Samun Zaman Lafiya Da Ci Gaba Ba Tare Da Nuna Fin Karfi Ba
- Rasha Ta Bayar Da Gawarwakin Sojojin Ukraine 1,000
Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson ya fitar, Jaridar PUNCH ta samu, ta ce, taron zai yi nazari a kan zaben cike gurbi da aka yi a baya-bayan nan, da kuma yin gangamin kira ga jama’a domin su fito su yi rajista da jam’iyyar. Jam’iyyar za ta kuma yi nazari kan batun sake duba kundin tsarin gudanar da ita kan muhimman batutuwan da suka shafi kare dimokuradiyyar kasa.
Har ila yau, jam’iyyar NNPP na iya goyon bayan sake tsayawar takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
“Har ila yau, jam’iyyar NNPP a bude take ga wasu zabuka uku: kulla kawance da sauran jam’iyyun adawa, ci gaba da zama a matsayin NNPP, ko kuma ta goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tsayawa takara.” In ji Johnson.
Sanarwar ta kara da cewa, “Za a tattauna wadannan zabuka guda uku a taronmu NEC a ranar 28 ga watan Agusta 2025. Don haka muna kira ga daukacin mambobinmu da su kwantar da hankalinsu, domin za a yanke hukunci na karshe domin amfanin jama’a.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp