Hukumar EFCC ta kama daraktoci biyu na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka tanadar don aikin Hajjin 2025.
Jami’an EFCC sun ce har yanzu suna tsare da su saboda sun ƙi mayar da kuɗin da aka umarce su da su dawo da su.
- An Gano Karin Gawarwaki 3 Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Fasinjoji 26 A Sokoto
- Kasar Sin Ta Zama Jagora Mai Haskawa Duniya Sabuwar Hanyar Samun Zaman Lafiya Da Ci Gaba Ba Tare Da Nuna Fin Karfi Ba
Sai dai ba a bayyana adadin kuɗin da ake magana a kai ba.
NAHCON ta fitar da sanarwa ta bakin kakakinta, Fatima Usara, inda ta ce hukumar na goyon bayan gaskiya da adalci, kuma ba za ta rufe idanu kan duk wani ma’aikaci da aka samu da laifi ba.
Ta ce suna aiki tare da hukumomin yaƙi da cin hanci domin tabbatar da gaskiya da bin doka.
Hukumar ta kuma roƙi jama’a da kafafen yaɗa labarai da kada su rinƙa yaɗa hukunci kafin kammala bincike.
NAHCON ta ce babban burinta yanzu shi ne duba yadda aka gudanar da aikin Hajjin, yin gyare-gyare, da kuma inganta wa alhazai tsarin Hajji a nan gaba.
Wannan na zuwa ne bayan wani bincike a 2024, inda tsohon shugaban NAHCON, Jalal Arabi, aka tuhume shi da karkatar da Naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar a matsayin tallafin Hajji.
Shugaba Bola Tinubu daga baya ya tsige shi daga muƙaminsa ya kuma naɗa Farfesa Abdullahi Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp