Aƙalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu a hare-haren ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Ɗan majalisar jihar da ke wakiltar Malumfashi, Hon. Aminu Ibrahim, ya shaida wa majalisar dokokin jihar cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 30 da ke salla sannan suka ƙone mutane 20 da ransu a sabbin hare-haren da aka kai a ƙauyukan mazaɓarsa.
- An Tsare Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
- Dole Ne Fasinjoji Su Kashe Wayoyinsu Gaba Ɗaya Kafin Jirgi Ya Tashi Ko Sauka – NCAA
Hare-haren sun faru ne a Gidan Adamu Mantau, Unguwar Yar Mai Dabo, Makera da kuma Burdigau.
Ibrahim ya ce lamarin ya bar jama’a cikin tsoro da baƙin ciki.
Ya bayyana cewa mazauna ƙauyukan sun yi kira da aka kai musu ɗauki kan hare-haren‘yan bindiga a kusa da Burdigau da misalin ƙarfe 6 zuwa 7 na yamma a ranar Litinin, amma sojoji sun iso daga baya suka kuma tafi ba tare da tsare yankin ba.
Da safiyar ranar Talata, sai ‘yan bindiga suka kai farmaki Unguwar Mantau tare da buɗe wasu mutane da ke sallar Asubah wuta, inda suka kashe mutum 30.
“Lamarin ya zama abun baƙin ciki. Mutanenmu ba za su iya ci gaba da rayuwa a ƙauyukansu ba saboda waɗannan hare-hare marasa ƙarewa,” in ji Ibrahim, yana roƙon a kafa sansanonin sojoji a Karfi da Yaba.
Jawabin nasa ya tayar da hankali a tsakanin sauran ‘yan majalisa, waɗanda suka nuna cewa kisan gilla yana ƙaruwa a Katsina duk da ayyukan da sojoji ke yi a jihar.
Mazauna Malumfashi sun roƙi gwamnatin jihar da ta tarayya da su ɗauki matakin gaggawa.
A baya an tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe masallata 13 ne a Unguwar Mantau da safiyar ranar Talata.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya shaida wa ‘yan jarida cewa gwamnati ta bayar da umarnin ƙara tsaro tare da kai wa waɗanda abin ya shafa tallafi.
“Lamarin ya faru ne lokacin da miyagu suka kai harin ramuwar gayya kan al’umma. Mutane na unguwar suna cikin masallaci suna sallar Asuba lokacin da miyagun suka fara harbe-harbe a cikin masallaci,” in ji Dr. Mu’azu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp