Wani matashi dan shekara 43 da ake zargin dan Kasar Indiya ne mai suna Sumit Sood, wanda aka kama bisa zargin satar wasu dalibai uku na makarantar Bishop Cotton School da ke gundumar Shimla, da farko ya yi kokarin dora laifin a kan wasu ‘yan kungiyar asiri na Nijeriya, kamar yadda jaridar PUNCH Metro ta ruwaito.
A cewar jaridar The Indian Edpress, ‘yansanda sun ce bayan sace daliban, Sood ya yi kira ta hanyar lambar waya ga iyayensu, yana mai nuna cewa “gungun ‘yan Nijeriya ne” suka tilasta shi ya nemi kudin fansa.
- Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan Maye Na Miliyan 680 A Katsina
- Jihar Xizang Ta Baiwa Duniya Mamaki Da “Canji Mai Girma” Da Ta Samu a Cikin Shekaru 60 Da Suka Gabata
An yi zargin cewa ya ba da umarnin a biya kudin fansa a cikin Bitcoin kuma ya gargadi iyayen “ka da su sanar da kowa, musamman jami’an makarantar, idan ba haka ba ‘yan kungiyar za su cutar da yaran da shi.”
Shimla Sufeto na ‘yansanda, Sanjeeb Gandhi, ya shaida wa jaridar The Indian Edpress cewa, “An yi wannan kiran ne ta manhajar TedtMe. Wanda ake zargin ya so a biya kudin fansa a Bitcoin.
“Binciken wayar salular Sood ya nuna cewa ya bincika kuma ya bincuke shafukan intanet sama da dozin uku, tashoshi na labarai na gida, da intanet BCS don duba ko labarin sacewar ya yadu.”
Gandhi ya kara da cewa lokacin da Sood ya samu labarin da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar cewa rahotannin daliban da suka bata sun bayyana, “ya yi shirin dauke su daga kauyensa Kokunala zuwa Chandigarh.
“Sood ya ajiye daliban a gidansa mai hawa uku da ke Kokunala saboda wurin da yake da nisa.” “Babu kowa a gidan lokacin da ya kawo su. Kafin ya aikata laifin, Sood ya sace bindigar mahaifinsa mai lasisi.”
Da yake karin haske game da motsin wanda ake zargin kafin yin garkuwa da shi, SP ya ce, “A daren da ya gabata, ya zauna a gidan kakaninsa da ke Ram Bazar na Shimla.
“Ya kauce wa CCTB ta hanyar daukar hanyar Bemloi-New Shimla kuma ya jira fiye da sa’o’i hudu a cikin motarsa, dauke da farantin karya, wanda ya ajiye kimanin mita 100 daga kofar makarantar. Har ma ya yi fitsari a cikin kwalbar a cikin motar.”
A yayin sake gina wurin da ake aikata laifukan, ‘yansanda sun ce Sood ya gano wurin da ke kusa da Dhalli inda ya rufe idanuwan dalibai uku, inda ya canza lambar motarsa, da kuma hanyoyin da ya bi ya isa gidansa na Kokunala da ke kusa da Kotkhai a ranar 9 ga watan Agusta. An shirya Sood zai gurfana a gaban kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp