Firayim ministan kasar Sin Li Keqiang, ya aike da wasikar taya murna, ga dandalin tattaunawa a fannin kirkire-kirkire na Pujiang na shekarar 2022 a jiya Asabar.
A cikin wasikar, Li Keqiang ya bayyana cewa, rage gurbatar iska, yana da nasaba da makomar duniya mai kiyaye muhalli a nan gaba, kuma kirkire-kirkire babbar hanya ce ta jagorantar samun ci gaba.
Li Keqiang ya yi nuni da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta dauki hanyar samun ci gaba, tare da rage gurbata iska, a yayin da take kokarin tabbatar da zamanantar da al’amura.
Ya ce hakan shi ne irin sa na farko a tarihin dan adam, kuma yana bukatar kwazo matuka don cimma nasara. Kasar Sin za ta yi la’akari da albarkatun da take da su, don kara amfani da kirkire-kikire a fannin kimiyya da fasaha, da inganta amfani da makamashi, da samarwa, da bunkasa fasaha, da yin kwaskwarima kan tsare-tsare, da nufin tabbatar da samar da makamashi yadda ya kamata, da aiwatar da ayyukan cimma burin kaiwa kololuwar fitar da hayaki mai dumama yanayi kafin shekara ta 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito, na yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan tasirin hayakin kafin shekarar 2060.
Baya ga haka, Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin tana nacewa ga babbar manufarta ta bude kofa ga waje, da sa kaimi ga yin gyare-gyare masu zurfi, da samun bunkasuwa mai inganci, bisa ga manufar bude kofa ga kasashen waje, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa ta kowane fanni, da zurfafa mu’amala da koyo daga juna, da cimma moriyar juna, da samun nasara tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)