Albarkacin taron koli na 25 na shugabannin kasashe membobin Kungiyar Hadin Kai Ta Shanghai (SCO), rukunin gidan rediyo da talibijin na Sin wato CMG, da sakatariyar kungiyar SCO sun shirya wani bikin hadin gwiwa na mu’ammalar al’adu a yau Litinin a Beijing.
Shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da firayim ministan Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif sun aike da sakon taya murnar cimma nasarar bikin. Kazalika, fitattun mutane daga fannonin siyasa, al’adu, da kafofin watsa labarai na kasashen SCO sama da 100 sun halarci taron, sun kuma shaida kaddamar da ayyuka da dama na mu’ammalar al’adu tsakanin kasashen kungiyar.
Yayin taron, CMG da sakatariyar SCO sun yi musanyar takardun hadin gwiwa. Har ila yau, bangarorin biyu za su kafa hanyoyin sadarwa na dogon lokaci, don kara karfafawa da kuma zurfafa hadin gwiwarsu, musamman a fannonin fasahar zamani kamar ta AI da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp