Jirgin ƙasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari da safiyar ranar Talata, lamarim da ya jefa fasinjoji da dama cikin hatsari.
Hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya bar Abuja da ƙarfe 11 na safe a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
- Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds
- Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Wani fasinja da ya wallafa labarin a shafukan sada zumunta ya bayyana cewa fasinjoji sun na cikin firgici, inda mutane suka dinga gudu domin tsira da rayukansu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ba ta tabbatar da lamarin ba, kuma ba a san abin da ta haifar da hatsarin ba.
Har ila yau ba a san halin da fasinjojin suke ciki ba.
Jami’an tsaro sun isa wajen domin taimakawa wajen kwashe fasinjojin da kuma tabbatar da cewa babu matsalar tsaro a wajen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp