Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum hudu da ake zargin ‘yan fashi ne daga cikin wata kungiya mai mutane 20 da ta kai farmaki unguwannin Madina da Fadaman Mada a jihar a ranar 16 ga Agusta, 2025.
An samu ruwait cewa miyagun mutanen, dauke da bindigogi, adduna, wukake da sanduna, sun afka wa unguwannin da sassafe, inda suka kwace wa akalla mutum 10 kayayyaki masu daraja, ciki har da wayoyin hannu guda 14, talabijin guda biyu, kaya na maza guda biyu da kuma kudi Naira 100,000.
- NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano
- A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho
Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da cafke mutanen a cikin wata sanarwa da ya raba wa wakilinmu a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.”
Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.
“A nan gaba kadan, da misalin karfe 05:03 na dare a wannan rana, jami’an leken asiri da ke aikin sintiri suka kama daya daga cikin barayin, Ahmed Hassan, mai shekara 20, dan unguwar Tirwun, Bauchi, yayin da yake yawo a Warinje Hills da wayar hannu ta Gionee da aka kwace a hannunsa,” in ji shi.
A cewar sanarwar, bayanin da Hassan ya bayar ya taimaka wajen cafke sauran mutum uku: Ismail Isah mai shekara 18 (wanda aka fi sani da Masha), Uzaifa Abubakar mai shekara 19 (wanda aka fi sani da Damo), da kuma Abdulhamid Idris mai shekara 20.
Kayan shaidar da aka kwato sun hada da bindigar kera gida kirar rebolber, harsashi daya na 7.62mm, wuka, bindigar gida gajera (Dane gun), adduna guda biyu, da fitila.
“A lokacin binciken da ake yi musu, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ne ke da alhakin wasu ayyukan fashi da makami daban-daban a cikin Birnin Bauchi. Ana ci gaba da kokari don bin diddigin sauran abokan harkarsu da kama su. Bayan kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Wakil.
Wannan cigaban ya biyo bayan karin matakan da ake dauka wajen yaki da aikata laifuka a jihar. A baya-bayan nan, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Sani Omolori-Aliyu, ya bayyana cewa an kama mutane 748 da ake zargi da hannu a cikin laifuka 394 a Bauchi cikin watanni takwas da suka gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp