Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jihar Legas ta samu amincewar ayyuka daga gwamnatin tarayya da suka kai darajar Naira tiriliyan 3.9, adadin da ya fi gaba ɗaya abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Gabas. Wannan ya tayar da cece-kuce kan batun adalci da daidaituwar raba kuɗaɗen ci gaban ƙasa.
Binciken ya nuna babban giɓin da ke cikin rabon kasafin ayyukan ci gaba a Nijeriya. Duk da cewa Legas kaɗai ta samu ayyuka da darajar tiriliyan 3.9, jihohin Kudu maso Gabas (N407.49bn), Arewa maso Yamma (N2.7trn), da Arewa maso Gabas (N403.98bn) sun raba jimillar tiriliyan 3.56. Yankin Kudu maso Yamma, wanda Legas ke ciki, ya fi kowa samu da jimillar tiriliyan 5.97, da suka haɗa manyan ayyuka irin su Lagos-Calabar Coastal Highway da gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ya kai Naira biliyan 712.
- ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro
- ADC Tana Da Damar Kayar Da Tinubu A Zaɓen 2027 – Amaechi
Sai dai gwamnatin tarayya ta ƙaryata zargin nuna bambanci. Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ya bayyana cewa shirin Renewed Hope Agenda na Tinubu yana tafiya bisa tsarin adalci, inda ya nuna ayyuka irin su hanyar Sokoto-Badagry da jiragen ƙasa a Kano da Kaduna a matsayin hujja na aikin “ci gaban ƙasa baki ɗaya.”
Amma masu suka na ganin lambobin sun tabbatar da akasin hakan. Wani Jigon PDP, Timothy Osadolor, ya zargi Shugaban ƙasa da yin mulkin ƙabilanci fiye da na ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa sauran yankuna suna samun “ragowar ci gaba.” Haka kuma, mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Auwal Rafsanjani, ya soki doka da tsarin kashe makudan kuɗaɗe ba tare da tsayayyen kasafi ba, yana mai danganta matsalar da “tsarin da ke tsotsar gumin wasu” wanda ke haddasa rashin ci gaba da jin cewa ana nuna wariya.
Wannan bincike ya sake fito da tsohon ƙalubale a tsarin mulkin Nijeriya: yadda za a daidaita muhimmancin raya cibiyoyin tattalin arziƙi irin su Legas da kuma wajabcin adalci wajen rabon arzikin ƙasa.
Yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tura manyan ayyukan ci gaba zuwa Legas, tambaya a nan shi ne: shin za a ji daɗin “Renewed Hope” daidai da yadda ake ji a bakin tekun Legas a ƙauyukan Arewa maso Gabas?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp