Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Ibadan North-West/Ibadan South-West a majalisar wakilai, Adedeji Olajide (wanda aka fi sani da Odidiomo), ya bayyana cewa zai siya wa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, fom ɗin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2027.
Olajide, wanda ya ke ɗan PDP ne a majalisa zangon na biyu, ya ce PDP ta riga ta kintsa shugabancin ƙasa zuwa yankin Kudu, kuma a cewarsa Makinde shi ne ɗan takara mafi cancanta da zai iya tsayawa da ƙarfin siyasar Shugaba Bola Tinubu.
- Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
- PDP Ba Za Ta Damu Da Rashin Atiku Ba – Gwamna Makinde
A cewar Olajide, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan fasahar sadarwa da tsaro ta yanar gizo, Gwamna Makinde ya cancanci tsayawa takarar shugabanci saboda ilimi, da kwarewar siyasa,da gogewar kasuwanci, da fahimtar duniya da kuma rawar da ya taka a matsayin gwamna na wa’adi biyu. Ya ce Makinde shi ne sabon fuskar siyasar Nijeriya.
Ya ƙara da cewa tasirin siyasar Makinde a PDP da ma ƙasa baki ɗaya ya sanya shi zama zaɓin da ya fi dacewa wajen jagorantar adawa zuwa ga nasara. Haka kuma ya bayyana salon mulkin Makinde da ya daidaita gina ababen more rayuwa da jin dadin jama’a a matsayin abin koyi ga siyasa mai ma’ana.
Olajide ya yi kira ga Makinde da ya bayyana niyyarsa cikin gaggawa, yana mai cewa lokaci ya yi da za a samu sabon salo na jagoranci a Nijeriya. Ya yi iƙirarin cewa Makinde shi ne kaɗai babban masallacin karfi daga Kudu maso Yamma da zai iya fuskantar Tinubu a zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp