Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622.
Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata a lamarin. Rahotanni sun nuna cewa asibitoci da dama, musamman na lardin Asadabad, sun cika da marasa lafiya. Shugaban asibitin, Dr Muladad, ya bayyana cewa suna karɓar marasa lafiya daga girgizar ƙasar “a duk bayan minti biyar,” kuma mutane 188 cikin sa’o’i kaɗan aka kawo asibitin, ciki har da mata da yara.
- Ya Zama Wajibi Amurka Ta Sauke Nauyin Dake Wuyan Ta Game Da Kasar Afghanistan
- Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci
Sai dai hukumomi sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar yawan mutanen da suka mutu zai ƙaru, kasancewar yankin da abin ya shafa mai nisa ne, kuma ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na fuskantar cikas wajen isa wurin.
Girgizar ƙasar ta auku ne da dare lokacin da mutane suke barci a gidajensu. Rahotanni sun nuna cewa daruruwan mutane na iya kasancewa sun maƙale ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe, lamarin da ke ƙara tsananta fargaba da damuwa a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp