Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a rungumi akidun tabbatar da daidaito da adalci, tare da tsayawa tsayin daka kan tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, da kara azamar inganta rayuwar al’umma a ko da yaushe.
Shugaba Xi ya yi kiran ne a yau Laraba, yayin bikin taron tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya.
Xi ya ce, shekaru 80 da suka shude, bayan shafe shekaru 14 ana gwabza kazamin yaki, al’ummar Sinawa sun yi nasarar murkushe dakarun mamaya na kasar Japan, tare da ayyana cimma cikakkiyar nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan muhimmiyar gaba ta tarihi ta sanya al’ummar kasar Sin ficewa daga zurfin tashin hankali tun shiga zamanin wayewar kai zuwa matakin farfadowar kasa, ya kuma kasance muhimmin lokaci na samun ci gaban duniya. Wannan muhimmiyar nasara ta samu ne ta hanyar hadin gwiwar Sinawa da sauran kawaye masu rajin kin tafarkin murdiya da sauran al’ummun kasashen duniya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, salon zamanantarwa irin na Sin, na kan tafarkin neman ci gaba bisa lumana. Kuma Sin za ta ci gaba da kasancewa babban karfi na wanzar da zaman lafiya, da daidaito da ci gaban duniya. Kana da sahihiyar zuciya, tana fatan dukkanin sassan kasa da kasa za su koyi darasi daga tarihi, za su mutunta hadin kai, tare da hada hannu wajen ingiza zamanantar da duniya da samar da makoma mai haske ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp