Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga watan Satumbar 2025, a matsayin ranar hutu don bikin ranar Mauludin Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
- Jihohi 18 A Arewa Za Su Iya Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Satumba – NiHSA
- Xi Jinping Ya Duba Faretin Rundunonin Sojoji Da Kayayyakin Soja, Shugabannin Kasashe 26 Su Ma Sun Halarci Bikin
Tunji-Ojo ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin a Nijeriya da sauran sassan duniya, yana mai kira a gare su da su yi koyi da halayen Annabi na zaman lafiya da soyayya da haƙuri da kuma tausayi.
Ya jaddada cewa irin waɗannan dabi’u ne ginshiƙan gina ƙasa.
Ministan ya kuma buƙaci ‘yan ƙasar nan, ba tare da la’akari da addini ba, da su yi amfani da wannan dama wajen roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali.
Ya ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da kula da tsaro tare da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa.














