• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

byShehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
1 month ago
Manzon Allah

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ta’ala wa Barkatuhu. Mun gode Allah, mun gode Allah, mun gode Allah, da Allah ya nuna mana wannan lokaci da za mu tattauna a kan wannan abu mai girma a addininmu, mai girma a rayuwarmu, mai girma a lamarin lahirarmu ma, shi ne mauludin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Sallama na bana wanda ya dace da cikar Manzon Allah shekara 1500 da haihuwa. To wannan abu ne mai girma kwarai da gaske. Duk wanda Allah ya sa ya riski wannan lokaci abin ya yi murna ne, abin ya yi godiya ga Allah (Tabaraka wa Ta’ala) ne da Allah ya raya shi, Allah ya shirya shi ya zo wannan lokaci.

Akwai wadanda su sun riski haihuwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa Sallama) din ma, sun riski zamanin. Akwai wadanda suke ta neman su riski zamanin ma kafin zamanin ya zo, yana daga cikinsu Annabi Ibrahim (AS), Allah ya fada mana addu’a yake yi ma Allah ya kawo wannan zamani, Allah ya kawo wannan haihuwa ta Manzon Allah (SAW).

  • Dakarun PLA Sun Gudanar Da Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin
  • Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Sallama mai girma ne a wajen Mahaliccinsa, kuma mai girma ne a wajen bayin Allah saboda shi ne karshen ma’aika wadanda Allah ya rika aikowa, don ci gaban ‘Yan Adam. Duk lokacin da zamani ya yi nisa, sai Allah ya aiko wani Annabi wanda zai yi daidai da al’ummar wannan zamani da kuma ilImin da zai yi daidai da wannan zamani. Idan an yi maganar Annabi an yi maganar ilmi, idan an yi maganar Ma’aiki an yi maganar sako daga Allah wanda babu hannun kowa a ciki.

A matsayinsa na Annabi kuwa ilimin da Allah ya ba shi, ya ba shi ne don ya gwada ilmin nan nasa ya karantar da su, ya gwada ilimin nan na sa ya yi komai, to a cikin gwada ilimin nan nasa wani lokaci za ka ga wani dan kuskure ya dan samu kadan sai, Allah ya kira wo shi a matsayin Annabin nan ya ce masa me ya sa aka yi kaza? Ko gyara kaza, amma Allah bai taba kiransa (wannan Annabin) a matsayin Ma’aiki ya ce me ya sa aka yi kaza ba? Domin ai ba shi da nasa, shi dan sako ne. Amma duk abin da Allah zai ce “me ya sa aka yi kaza?” ko “a gyara kaza” za ka ga ya ce “ya kai wannan Annabi”, amma wajen ma’aiki kuwa sako ne kawai ba shi da nasa.

Aiken Annabi Nuhu (AS) shi ne cewa a bauta ma Allah, a girmama iyaye, wannan sako ne na Allah ga baki daya, babu nasa a ciki. Amma kuma yanzu ga halaka za ta zo, za a yi ruwan dufana, za a yi mamakon ruwa, to kuma yanzu a gina jirgin ruwa a yi dabara yadda ruwa ba zai shiga cikin jirgin nan ba, yanda zai nemi iyakar mabiyansa, yadda zai tseratar da wasu daga cikin dabbobi; yanzu kuma a matsayinsa na Annabi, a matsayinsa na Malami ne wannan. Ga kira zuwa ga Allah a matsayinsa na Ma’aiki, ga kera jirgin ruwa a matsayinsa na Annabi.

LABARAI MASU NASABA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

To Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, a matsayin aike shi ne karshe, shi ya zo da aike na karshe, wanda daga shi aiken Allah (Tabaraka Wa Ta’ala) ya kare. Sai dai na Manzon Allah (SAW) din nan ne za a yi ta bincikawa a yi ta gani saboda na Manzon Allah din nan yanzu ya dace da kowanne zamani. Ubangiji Tabaraka wa Ta’ala shi ne mai cikakken ilimi, shi ya halicci ilimi ma. Allah shi ne farko kanta, shi ne karshe kanta, shi ne a sarari kuma shi ne a boye, ma’ana ya san komai ciki da bai, don haka a wannan matsayi nasa ya zuba ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam wannan ilimai a cikin wannan littafi na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Galibin Annabawa kowa Allah yana aiko shi da iyakar ilimi da ya yi daidai da zamaninsa, duk idan muka duba a Alkur’ani za mu ga kowanne Annabi da irin kiran da ya yi. Cewar “a bauta ma Allah shi kadai” wannan na dukkan Annabawa ne, amma kuma za ka ga wani ya yi kira zuwa ga girmama iyaye, wani ya yi kira zuwa a yi awo da adalci, wani ya yi kira zuwa a yi tsarki, da sauransu, har aka zo kan Annabi Musa (AS) shine Mai Shari’a “Al-Kitabu”.

Allah ya ba Annabi Musa “Constitution” na abubuwa mai hukunce-hukunce wajen dari shida da wajen goma sha uku. Duk abinda Annabi Musa yake kai, da duk abin da zamaninsa yake kai sai da Allah ya rubuce masa shi a cikin Attaura. Kuma ya yi masa dalla-dallansa, sannan ya fitar da wadansu kyawawan dabi’u ya sanya masu suna “wasiyyoyi guda goma” (The Ten Commandments), su ma a cikin littafin suke amma saboda muhimmancin su ya sa Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya ware su daban. Amma wannan sako na Attaura iya na wannan zamanin ne, iya na al’ummar Annabi Musa ne (Yahudu), ba zai zama har abada ba. Don haka da Annabi Isah (AS) ya zo sai ya gaya masu “to Ni kam Allah ya aiko Ni in saukaka wadannan hukunce-hukunce na Annabi Musa”. Kamar yanda shi ma Annabi Musa Allah ya saukaka masa ne daga hukunce-hukuncen Hamuraabi; wani sarki da aka yi a Babylon, kasar Iraki. Kila shi ma Annabi ne, kila Bawan Allah ne, amma dai Sarki ne kasaitacce wanda shi ya kafa dokoki masu yawa a cikin tsararensa na mulki (Constitution). Akwai kisa da yawa a cikin hukunce-hukuncensa, amma Allah sai ya sanya ma Annabi Musa kisa goma sha takwas kawai. Amma da Annabi Isah (AS) ya zo, shi kuma yanzu kiransa ba iyakar Bani Isra’ila (al’ummar Annabi Musa) kadai ba ne, Annabi Isah (AS) yana so ya fadada kiransa zuwa ga halitta baki daya, wanda kuwa yake son irin haka to dole hukunce-hukuncensa su zama masu sauki kuma masu kyau.

Ko su hukunce-hukuncen masu tsauri na Attaura da aka sanya ma Bani Isra’ila an sanya masu ne saboda zaluncinsu. Shi kuwa Annabi Isah (AS) da ya zo sai ya ce ma Bani Isra’ila ku yi imani da ni, ni kuwa zan dan saukaka maku wani abu daga cikin wadanda aka haramta maku. Akwai wani wa’azinsa da ya yi a majami’a (temple) da dare, ya ce masu: “a Attaura ta ce muku kaza ni kuwa na ce muku kaza, a Attaura ta ce kar ku ci kaza, ni kuwa na ce ku ci babu wani abu da zai shiga cikin Dan Adam da zai gurbata Dan Adam din nan, shi dan Adam maganarsa da take fitowa daga cikinsa da kuma mummunan kudirinsa su ne suke gurbata shi.

Don haka za ka ga mabiyan Annabi Isah ba su da wani abu na ci da yake haram, domin ya ce shi bai ga wani abu daga waje wanda zai shiga cikin Dan Adam ya gurbata shi ba, sai dai abin da yake cikin Dan Adam din ne kawai zai iya gurbata Dan Adam, ma’ana shi Dan Adam din ne najasar da kansa, domin daga cikinsa maganganun batancin suke fitowa. Sai Annabi Isah (AS) ya ce ma jama’arsa “amma kun ga Annabi Ahmadu (SAW) da zai zo, shi kuwa zai zubar muku da duk abubuwan da aka hana maku din nan gaba daya, zai zubar da duk wani kunci”. Amma idan mai tambaya ya tambaye ka to ya aka yi na ga Haram a cikin addinin Annabi Muhammad (SAW) masu tarin yawa? Amsar ita ce wannan duk aikin malamai da fakihai ne, su ne suka sanya mafi yawancin haramun din cikin addinin nan namu tun daga kan Sahabbai (Allah ya yarda da su) zuwa Tabi’ai zuwa abin da ya yi kasa, akwai su “Sadduz Zari’ati” akwai haramta duk wasu hanyoyi wadanda sai idan ka biyo ne sannan za su iya kai ka ga aikata laifin. To Alhamdu Lillahi, yanzu zamani ya kawo, ko ka zama Annabi Isah din; ka zubar da kadan, ko kuma ka zama al’ummar Annabi Muhammadu; ka zubar da gaba daya! Kur’aninka dai yana nan ya fada maka komai gaba daya.

Annabi Isah (AS) ya zo da abubuwa masu sauki, ya yada littafan da suka zo kafin sa, Allah ya sanya sauki a cikin lamarinsa, Allah ya sanya sauki a cikin mutanensa, don haka ‘Yan Adam suka karba, amma saboda sauki (domin duk abu in ya yi sauki to ya zama na ‘Yan Adam baki daya, haka kuma duk abu in ya yi tsauri to iya naku ne). Daga nan har Allah ya kawo Bulus, wanda almajirin Annabi Isah din ne, shi kuwa Bulus gaba daya ma sai ya watsar da dokokin Attaurar ma, sai ya dauki “wasayal ashri” din nan, kawai abin da ya dauka a cikin Attaura kenan. To mu ma ikon Allah, wannan “wasaya” guda goma Allah ya tafi da su a cikin Kur’aninmu, ita ce “Furkánu”.

To, amma idan muka zo wajen Annabi Muhammad (SAW) wanda shi ne karshen ma’aika, shi kuwa Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya tattaro karatun fasahar “Engineering” din gaba daya ya damka masa (SAW). Duk littafin tafsirin da ka duba za ka ga ana yin sa ne daidai da wayewar al’ummar lokacin amma Alkur’anin kansa na farko ne na karshe ne, wata fahimtar ma tasa ba ta zo ba sai nan gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Kyawawan Abubuwa Da Allah Ya Yi Wa Manzon Allah (SAW) Na Girmamawa
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah

August 29, 2025
Next Post
uba sani

Gwamnatin Kaduna Ta Zargi El-Rufai Da Yunkurin Tayar Da Tarzoma A Jihar

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version