Yayin da duniya ke bikin watan wayar da kan yara kananan, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa; akalla yara 400,000ne ke kamuwa da cutar kansa a duk shekara a duniya, kwatankwacin yara uku a duk minti hudu.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta lura da yadda ake samun banbanci a tsakanin masu dauke da cutar, domin kuwa kashi 80 cikin 100 na yara a cikin kasashe masu tasowa, suna tsira daga cutar kansar, idan aka kwatanta da daya cikin biyar na matalautan kasashe da kuma tsaka-tsaki. Hukumar ta bayyana wannan a matsayin “daya daga cikin mafi girman rashin daidaito a bangaren da shafi cutar kansar.”
Da yake magana a wani taron masu ruwa da tsaki na yara kanana a Masar, wadanda suka tsira sun bayyana yadda suka sha fama da cutar. Daya daga cikin wadanda suka tsiran, ya bayyana wa mahalarta taron cewa; “Cutar ta yi yunkurin hallaka ni, amma taimakon likitoci da dangina da kuma abokaina ne ya karfafe ni. Ga shi a yau ina karar da labarina, ni da kaina.”
Taron, wanda Ministan Lafiya na Kasar Dakta Khaled Abdel-Ghaffar ya kaddamar, ya hada da kwararru da wadanda suka tsira da ransu, wadanda suka yi kira da a dauki matakan gaggawa, domin tseratar da rayuka.
A shekarar 2018, Hukumar Lafiya ta Duniya da Cibiyar Nazarin yara, sun kaddamar da kungiyar GICC da manufar habaka ceto rayukan yara kanana da kashi 60 cikin 100 daga nan zuwa 2030. Duk da kalubale irin daban-daban da suka shafi rikice-rikice da karancin lafiya, ana samun ci gaba a kasashe da dama karkashin tsarin kulawar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya.
Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp