Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin ƙungiyar ma’aikatan mai da iskar gas ta ƙasa (NUPENG) da kamfanin matatar Dangote, tana roƙon ƙungiyar da ta dakatar da yajin aikin gama garin da ta shirya fara wa a ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya tabbatar da cewa ya kira taron sasanci na gaggawa da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa a Abuja.
- NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
- Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON
Sanarwar da sashin yaɗa labarai na ma’aikatar ya fitar ta ce ministan ya roƙi NUPENG da ta janye shirin shiga yajin aiki tare da neman ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ta janye gargaɗin da ta aika wa rassanta. Ya ce tun da gwamnati ta shiga tsakani, akwai buƙatar a bai wa tattaunawa dama.
Dingyadi ya gargaɗi cewa yajin aiki a sashin mai zai iya jefa al’umma cikin mawuyacin hali tare da jawo asarar kuɗaɗe masu yawa ga gwamnati. A cewarsa, “Sashin mai yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar nan. Yajin aiki ko da na kwana ɗaya zai jawo babbar illa.”
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta tabbatar da an cimma matsaya mai gamsarwa ga dukkan ɓangarorin da rikicin ya shafa, yana mai jaddada cewa manufar gwamnati ita ce samar da lumana da kuma guje wa halin da zai kawo wahala ga ƴan ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp