Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya zargi jam’iyyar APC da amfani da ’yan daba wajen kai wa ‘ya’yan jam’iyyar ADC hari.
Malami ya ce an kai wa tawagar ayarinsa hari a Kebbi, haka kuma an kai wa Malam Nasir El-Rufai hari a Kaduna da Gbadebo Rhodes-Vivour a Legas.
- Ana Zargin Jami’in Sibil Difens Da Harbe Abokin Aikinsa A Abuja
- Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye
Ya bayyana cewa wannan na nuna an shirya tsari na amfani da tashin hankali domin hana su yin adawa da gwamnati.
Ya yi wannan magana ne bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai masa ziyara a Abuja domin nuna masa goyon baya.
Malami ya ce dimokuraɗiyya ba ta dogara da tashin hankali ba, sai dai tattaunawa, gaskiya da mutunta juna.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna bambanci ba.
A cewarsa, hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa barazana ce ga makomar dimokuraɗiyya a Nijeriya, don haka dole a yi magana a kai kafin abin ya zama al’ada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp