Tsohon Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya bayyana a hedikwatar EFCC da ke Abuja a ranar Laraba don amsa tambayoyi kan aikin gyaran matatun mai na dala biliyan 7.2.
Kyari ya isa ofishin da misalin ƙarfe 2:15 na rana bayan an gayyace shi don bayyana batutuwan kuɗi da suka shafi lokacin da yake shugabantar kamfanin man fetur na ƙasa.
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- Shettima Ya Yaba Wa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Ƙwarewa Ta Jihar Kaduna
Wannan lamari ya biyo bayan umarnin wata kotu na toshe wasu asusun banki guda huɗu da ake zargin suna da alaƙa da shi kan badaƙalar.
Masana sun ce bayyanar Kyari a EFCC na nuna cewa hukumar tana ɗaukar matakan da suka dace wajen yaki da rashawa a fannin man fetur da gas a Nijeriya.
Kyari bai yi tsokaci kan zargin ba, amma bayyana kansa a hukumar ana ganin alamar haɗin kai ce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp