Wani masanin tsaro, Dr. Bulama Bukarti, ya karyata ikirarin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa gwamnatin tarayya tana biyan kudaden fansa tare da samar da kayayyaki ga ’yan bindiga da ke addabar Nijeriya.
El-Rufai ya yi wannan zargi ne a shirin Sunday Politics na tashar Channels TV, inda ya dora alhakin tabarbarewar tsaro a kan gwamnati.
- Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 10 A Jihar Neja
- DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci
Sai dai a martaninsa, Dr. Bukarti ya ce kalaman El-Rufai ba su da tushe, yana mai bayyana su da cewa “siyasa ce tsagaronta babu gaskiya.” Ya bayyana cewa babu wata doka ko manufa da ta bai wa gwamnati damar biyan ’yan bindiga ko kuma tallafa musu.
A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.
Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.
Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.”
Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu an taba yi a kan gwamnatocin baya ma.
Yayin da yake bayani kan tsarin rundunar sojoji. Bukarti ya jaddada cewa shugaban kasa ne kadai ke da ikon bayar da umarnin daukar matakin soja. Ya ce gwamnoni, ministocin tsaro da ma mai ba da shawara kan harkokin tsaro ba su da wannan iko. A cewarsa, tsarin umarni daga shugaban kasa yake farawa zuwa Babban Hafsan Soja, sannan daga can zuwa kwamandojin filin daga.
A ƙarshe, Dr. Bukarti ya ce magance matsalolin tsaro a Najeriya na bukatar dogon lokaci, hadin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da ’yan kasa, tare da tsaurara matakan yaki da cin hanci da rashawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp