Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (TUC) ta ƙi amincewa da shirin Gwamnatin Tarayya na ƙaƙaba wa man fetur harajin kashi 5, inda ta bayyana wannan shawara a matsayin “mugunta a fannin tattalin arziƙi.”
Yayin da ta ke kare wannan ƙudiri bayan bayani da Daily Trust ta yi a kan manufar, Gwamnatin Tarayya ta ce manufarta ita ce samar da tabbataccen kuɗi don ayyukan hanyoyi da kuma cike giɓin da ke akwai a fannin ababen more rayuwa a ƙasar.
- Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
- Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano
“Bari a fayyace komai: Ma’aikata da ƴan ƙasa har yanzu suna fama da raɗaɗin cire tallafin mai, hauhawar farashin man fetur, tashin farashin abinci, da faɗuwar darajar Naira. Yanzu kuma an kawo wani sabon haraji kan mai, wannan zai ƙara jefa al’umma cikin ƙuncin rayuwa da wahala, raunana kasuwanci, da zurfafa talauci ga miliyoyin ƴan ƙasa.
“Gwamnati ba za ta ci gaba da amfani da ƴan Nijeriya a matsayin saniyar tatsa don gwaje-gwajen tattalin arziki ba. Maimakon samar da sauƙi, ayyukan yi da mafita, ta zaɓi ƙara matse ƴan ƙasa gami da jefa su cikin ƙunci. Wannan abin da ba za a iya yarda da shi ba ne!”
TUC ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da wannan shirin da bata da fa’ida ga mutane baki ɗaya. Rashin yin hakan, a cewar ƙungiyar, zai tilasta ta tare da ma’aikatan Nijeriya da al’umma baki ɗaya yin adawa da gwamnati a ƙasa baki ɗaya.
A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.”
Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya.
“Tare, dole ne mu yi adawa da manufofin da ke ƙoƙarin ƙara talauci ga ƴan ƙasa da ɗora mana nauyin nan gaba. Lamarin ya isa haka. Ƴan Nijeriya na da haƙƙin samun sassauci ga lamarin da shafi tattalin arziƙi, ba a ci gaba da azabtar da su ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp