Wani ganau ba jiyau ba, mai suna Mustapha Badamasi, Ɗan Bakano da ke unguwar Tudun jukun ya bayyana cewa; an tsinto gawar mutum guda daga ambaliyar ruwan, inda kuma aƙalla mutum biyu suka ɓace, har yanzu ana ci gaba da neman gawarwakin nasu.
An samu gawar Yusuf Surajo, wanda aka fi sani da Abba, yayin da Fatima Sani Danmarke da ɗanta mai shekaru uku da haihuwa a duniya da kuma wani mai babur da har yanzu ba a gane ko wane ne ba.
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria
- Gwamnatin Kaduna Ta Umarci Makarantu Masu Zaman Kansu Da Su Nemi Amincewarta Kafin Ƙara Kuɗi
Wannan iftila’i, ya faru ne a babban titin Gaskiya, kusa da wani Coci a Tudun Jukun, inda ruwa ya yi awon gaba da wata babbar kwatar magudanar ruwa a gefen titi,” in ji shi.
Har ila yau, wani ganau ya bayyana cewa; wani direban babur ne jim kaɗan bayan ruwan sama ya ɗauke da wata da jaririnta, ɗan shekara uku; ya bugi bakin magudanar ruwan da ke gefen titin tare da yunƙurin afkawa ciki.
“Sai matar ta yi sauri ta tsallake daga kan babur ɗin, a lokacin da take ƙoƙarin haye magudanar ruwan da ƙafa; sai ta zame ta faɗi tare da ɗan nata da ke goye a bayanta, nan take ruwan da ke faman gudu ya yi awon gaba da su.
“Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa.
Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su.
Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa.
“Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi.
Kazalika, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an yi ƙoƙarin jin ta-bakin Shugaban Hukumar Bayar da Agaji Gaggawa ta Jihar (SEMA), na shiyyar Zaria, amma abin ya faskara; sakamakon rashin samunsa ta wayar tarho.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp