Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa ’yan kasuwa na cikin gida cewa jihar na kan wata sabuwar turba kuma tana samun ci gaba sosai, inda ta ke sauyawa daga jihar da ƙalubale suka mamaye ta.
Gwamnan ya ƙaddamar da rabon tallafin a ƙarƙashin shirin SABER (SERBS) a ranar Alhamis a sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja
- Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa shirin gwamnatin jihar kan kawo sauyi kan harkokin kasuwanci (SABER) na nuna da wani gagarumin ci gaba a habaka tattalin arzikin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara.
Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau da kullum, inda ya tabbatar da cewa adadin kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ayyukan shirin ya kai kusan Naira Biliyan 1.1, tare da tallafin da ya kai dalar Amurka miliyan 20 zuwa dala miliyan 52 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026.
“Mun taru ne a yau domin ƙaddamar da shirin tare da fara bayar da kuɗaɗe don tallafa wa ‘yan kasuwa da mata daban-daban a fafin jihar nan.
“Akwai manyan nau’o’i uku na kuɗaɗen da za a biya, mun yi nazari sosai kan cibiyoyin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda shugabannin ƙungiyar ‘yan kasuwa ke wakilta, don zabar waɗanda za su ci gajiyar kowane fanni na tallafin.
Gwamna Lawal ya ci gaba da jaddada cewa shirin na SABER wanda ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta shirya shi, ma’aikatu daban-daban ne ke aiwatar da shi, waɗanda suka haɗa da ma’aikatar kasuwanci da masana’antu, ZAGIS, da sauran su kamar kuɗi, noma, da shari’a. Hakanan ya ƙunshi ayyuka na Harajin Cikin Gida, Kamfanin Gidaje, da ZITDA, suna aiki tare don samar da sauƙin kasuwanci.
Tun da farko, Babban Darakta na Hukumar Raya Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu ta Nijeriya (SMEDAN), Charles Odii, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa ɗimbin ƙoƙarinsa na tallafa wa ‘yan kasuwa na cikin gida a Jihar Zamfara.
“Na ji daɗin yadda gwamna ke bakin ƙoƙarinsa wajen bunƙasa ƙananan sana’o’i a Nijeriya, ina zaune na ji cewa ‘yan kasuwa 2,000 za su samu Naira 150,000. Ina ganin yana da muhimmanci idan ƙaramin ɗan kasuwa ya samu Naira 150,000, zai ɗauki mutum ɗaya aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp