Hukuma kula da bada bashin karatu tace ta ba ɗaliban kwalejin ilimi ta tarayya ɓangaren fasaha ta Gombe bashin Naira milyan N32, 142,000.00 ga ɗaliban Kwalejin 750.
Kuɗaɗen ,an ba ɗaliban cikin watan Agusta ne abinda kuma ya kasance tsarin biyan kuɗin ne da aka yi domin, b a sauƙaƙawa ɗaliban matsalar biyan kuɗin makaranta da kuma al’mura nay au da kullun, ga ɗaliban da suka cancanta suka kuma nemi da a basu bashin.
- Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC
- Muna Fama Da Targade Sai Ga Karaya – ‘Yan Nijeriya
NELFUND ta bayyana hakan ne, ta kafar sadarwarta ta Ɗ (wato Twitter a lokacin daya gabata) ranar Asabar, ta bayyana cewa makarantar ta tabbatar da cewar kuɗaɗen sun shigo hannunta, ta hanyar wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun mataimakin Shugaban Kwalejin Dakta Mohammed Guzali Abdulhamid ranar 2 ga Satumba 2025.
Biyan kuɗin da ba’a daɗe ba yana da cikin tsarin da hukumar take yi dukkan makarantun da suka cancanta a sassa daban daban na Nijeriya, tun da yake hukumar ta ƙaddamar da tsarin nata na taimakawa wajen samun damar karatu a manyan makarantu domin samun ilimin gaba da Sakandare.
Bada daɗewa bane hukumar ta bada sanarwa ta biyan kuɗaɗenga ɗaliban da ke Jami’oi da Kwalejoji, yayin da take ƙara himma kan ayyukanta.
Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin
Hukumar ta kafar sadarwar zamani duk waɗanda suke amfana da tsari da su tabbatar da bayanan Banki da suka bada da na makaranta daidai suke domin hakan ne zai bada dama ta ci gaba da samun kuɗin duk lokacin da aka tashi biya ba ater da ɓata lokaci ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp