Fadar Shugaban Ƙasa ta soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa cewa ’yan Nijeriya na fama da yunwa da kuma tashin hankali.
Atiku ya kwatanta halin da ake ciki a Nijeriya da juyin juya halin Faransa na 1789 da na Rasha na 1917.
- Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
- Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Sai dai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar watsa labarai, Bayo Onanuga, ya ce maganganun Atiku ba daidai ba ne.
ya ƙara da cewa Nijeriya na samun ci gaba a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.
Onanuga ya yi misali da yadda bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) da suka nuna farashin kaya na sauka tsawon watanni biyar a jere.
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
“Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama. Ko da Atiku da magoya bayansa ba su yadda ba, ’yan Nijeriya suna ganin sauyin,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.














