Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewa ba zai bari kowa ya kawo katsalanda ko tsaiko ba a zaben 2023 da ke kara karatowa.
Buhari, ya ce shugabancin da ba a gina kan turbar gaskiya ba, ba zai kawo alfanu ga Nijeriya ba.
- Ficewar Malam Shekarau Daga NNPP: Me Ya Sa Hankalin ‘Yan Kwankwasiyya Ya Tashi?
- “Gwamnonin APC Ku Kwana Da Sanin Cewa Ba Zan Ce Uffan Ba A Zaben 2023” — Buhari
Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne lokacin da yake tarbar gwamnonin jam’iyyar APC da gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ke jagoranta a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban Nijeriyar ya kuma ce a karkashin shugabancinsa, zai ci gaba da mutunta ‘yan Nijeriya ta hanyar tabbatar da cewa kuri’unsu sun yi tasiri saboda suna da ‘yancin zabar shugabannin da suke so a dukkan matakai.
A cewar Buhari, wannan na daga cikin dalilin da ya sa ya yi gaggawar sanya wa dokar zabe ta 2022 hannu don yi mata garambawul.
Sannan ya ce a matsayinsa na shugaba ba zai sa hannunsa cikin abin da ya shafe zabukan da za a yi a 2023 ba, don a cewarsa ‘yan Nijeriya na damar zabar wanda suke so a matsayin shugaba.