Wata babbar kotun sojin Nijeriya dake zamanta a Maxwell Khobe dake Jos, ta yankewa wani soja, Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wani mai tuka keke-napep (Adaidaita) mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na jihar Bauchi.
Birgediya Janar Liafis Bello, Shugaban Kotu ta runduna ta 3 ta Sojin Nijeriya ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 18 ga Satumba, 2025, bayan kotu ta samu Musa da laifin kisan kai da kuma mallakar harsasai ba bisa ƙa’ida ba.
- Jose Mourinho Ya Zama Sabon Kocin Benfica
- An Bude Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Birnin Beijing
A cewar kotun, Musa, tare da abokin laifinsa mai suna Mista Oba, sun yaudari Isa (Mai keke-napep) zuwa gidansa da sunan taimaka masa wajen kwashe kayansa. Shaidun da aka gabatar a lokacin shari’ar sun nuna cewa, Musa ya bugawa Isa katako kafin ya shake shi har lahira. Daga baya, suka cusa gawar a cikin buhu aka jefar a tsakanin kauyukan Shira da Yala, sannan aka sayar da keke-napep ɗinsa.
Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba.
Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari. Bugu da ƙari, an kore shi daga aikin sojan Nijeriya acikin ƙasƙanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp