A satin da ya gabata, 4 ga watan Satumba, daidai da 12 ga watan Rabi’ul Awwal, Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Kaduna ta yi zaman murnar haihuwar Annabi Muhammad SAW wanda ya cika shekara 1,500 da haihuwa a bana. A wannan makon kuma, Zawiyar ta gabatar da zaman suna (Takutaha) na Annabi SAW a ranar 11 ga watan Satumba, 2025.
Manzon Allah SAW, yana da sunaye masu yawa da Ubangiji tabaraka wata’ala ya ambace shi da su acikin littattafan Annabawa da littafinsa (Alkur’ani), da kuma sunayen da aka samo acikin Hadisai. Ana cewa, yawan sunaye na nufin girman mai sunan (Kasratul asma’i tadillu ala sharafil musamma).
Manyan Malamai sun tattaro sunayen Annabi SAW, kowane iya kokarinsa. Daga cikinsu, akwai wanda ya tattaro sunaye 99 na Annabi SAW gwargwadon adadin na Ubangiji tabaraka wata’ala wadanda suka zo a Hadisi.
Alkali Iyad, mai littafin Ashafa, yana cewa, Allah ya kebe Annabi SAW, ya ambace shi da sunaye masu yawa, hatta Ubangiji da kansa ya kira Annabinsa da sunayensa kusan 30. Arra’ufu da Arrahimu duka sunayen Ubangiji ne amma ya kira Annabinsa da su acikin ayar “Lakad ja’akum rasulun min anfusikun… bil muminina RA’UFUN RAHIM”, wannan girma ne ga Annabi SAW.
Alkali Iyad, ya ci gaba da cewa, akwai sunaye kusan 70 na Ubangiji da ya kira bawansa, Annabi SAW da su, amma sauran Annabawan guda daya kacal ya ba su. Annabi Ismail, an ba shi Habibu; Annabi Ishak, an ba shi Habibu; Annabi Nuhu, an ba shi, Shakuru da dai sauransu.
Ibnu Mudi’a yake cewa, idan aka bincika cikin littattafan da suka gabata na Annabawa, da Alkur’ani da Hadisai, za a samu sunaye kusan 300 na Annabi SAW.
Abubakar ibnul Arabi Almaliki, ya ce, wasu daga cikin sufaye sun tattaro cewa, Ubangiji tabaraka wata’ala yana da sunaye 1000 haka ma Annabinsa.
Shihabuddin Askalani mai littafin mawahibul ladunniyya fi muna’il muhammadiyya, sai da ya tattaro sunayen Annabi SAW 400 ya zuba cikin wannan littafin na sa mai albarka (Allah ya yi masa sakayya da alkairi).
Imam Jazuli, acikin littafinsa mai suna “Dala’ilul kairati” sai da ya tattaro sunayen Annabi SAW 201 cikin sauki.
Imam Suyudi acikin littafinsa mai suna “Albahjatus sariyya”, ya tattaro sunayen Annabi SAW 500 acikin littafin.
Muradin wadannan sunaye, shi ne lafazuzzuka da suka nuna girmansa, hakurinsa da siffofinsa SAW.
Haka Diwanin Shehu Ibrahim Inyass Kaulaka, ya tattaro sunayen Annabi SAW da dama, a Harafi daya (Wasiktu), ya kawo sunaye kusan 70.
Bari mu lissafo kadan daga cikin sunayen Annabi SAW da Shehu Ibrahim Kaulaka ya ambato acikin wannan harafi na Wasiktu:
MAHIL KUFRI, mai share kafirci ko mai share zunubin al’ummarsa; AHMADA, mafi godiyar Allah; HASHIRI, wanda za a tashi al’umma a ranar Alkiyama bisa karkashin jagorancinsa; MUHAMMADU, sunan da aka fi saninsa da shi, ma’ana abun yabo, an ce da kakansa, meyasa ka ambace shi da wannan suna, sai yawce, don a gode masa a sama kuma a yabe shi a kasa, kuma Allah ya tabbatar da haka; ALMUKTARI, abun zabi; KAIRIL MA’ASHIRI, fiyayyen Dangi; MAHMUDI, abin yabo, dAHA, tsarkakakke. Shehu yake cewa, ina kan son Annabi matukar ina raye kuma har sai na jagoranci duk wani mai son Annabi SAW.
Annabi SAW ya zo AkIBAN, karshen Annabawa, shi aka ambata a farko kuma shi ne yazo a karshe, don babu wani Annabi bayansa; NURAN, haske ne; SIRAJAN, wanda ake dosanar haske daga wurinshi (fitila), duka Annabawa, Mursalai, Waliyyai da Mu’uminai daga haskensa suka samu hasken zuciya,kuma haskensa bai ragu ba; RAHMATAN, kyautaye ne kuma jinkai ga bayi, komansa Rahma ne, (Wama arsalnaka illa rahmatan lil’alamin – bamu aikoka ba, sai don ka zama rahma ga halitta), shi da kanshi yana cewa, “ni ne kyautar rahmar da Ubangiji ya baku”; mun gode Allah da ya bamu Annabinsa, Annabin Rahma.
RASULAN, ma’aiki ne; AMINAN, amintacce, wanda Ubangijinsa ya amince masa, ya turo shi da sako, kuma ya isar lafiya kalau, bai kara ba bai rage ba, amintacce ne a sarari da boye; SHAHIDAN, mai shaida ga halitta, Annabawa da al’ummatai, kuma ABDAL ILAHI, bawan Allah ne a fadar Ubangiji, shugaba ne a wurin ‘yan Adam. MUBASHSHIRAN, BASHIRAN, mai siffantuwa da Bushara, kuma yana umurtar duk Malamai da su zama masu Bushara, saukakawa ba tsanantawa ba, an yi daidai ba an yi kuskure ba, kusantarwa ba nesantarwa ba; NAZIRAN, mai gargadi da azzaluman halitta.
Annabi SAW ya zo Balarabe, UMMIYYUN; mai mira zuwa ga Allah, DA’IYAN; kuma Annabin da yazo mana da abun da babu wanda yazo mana da irin shi, shi ya zo mana da karshen Ilimi sai dai Malamai su yi ta warware suna fidda Ilimi. Kowane Musulmi ya yi imani da cewa, Alkur’ani ya dace da kowane zamani amma ba a iya ganin haka a aikace ba. Mu yi kokari muga irin wannan Imanin a zahiri.
MUkAFFA, MUSdAFA, BADRU, haskensa kamar wata dan daren 14 amma Jabiru, yace wallahi Annabi yafi watan dan daren 14 kyawu da haske; SHAFI’UL BARAYA, mai ceton halitta acikin masifa irin ta ranar Alkiyama.
Allah naka ne, ya Rasulullah, ba zan gushe ba ina yabon Manzon Allah SAW, shi ne URWATUL WUSkA, igiya mai karfi, wannan shi ne tanadi na.
NABIYYUN, annabi ne; KARIMUN, mai girma, komai na shi mai girma ne; MUTTAkIN, mai tsoron Allah ne; MUSLIHUN, mai gyara ne; IMAMUN jagora ne; RA’UFUN, mai tausayi ne; MUJTABAN, abun zabi ne; kuma NASIRI, mataimakin halitta baki daya.
Ya isarmin, shugabana ne, YASIN; MUkIMUN, mai tsayar da tafarki madaidaici; tafarkin addinin musulunci Hanafiyyi ne, ma’ana mai karkata zuwa ga tafarkin Ubangiji, ma’anar Hanafiyya ta asali, shi ne, tun zamanin Annabi aka saukar a Alkur’ani amma har wannan zamani kullum sabone kamar a yanzu aka saukar da shi, sabida mai sassauyawa ne da ilimin zamanin da ake, babu ranar da Alkur’ani zai tsufa sai dai mai Tafsirin ya tsufa. Sabida na Allah ne kuma Allah rayayye ne.
MUdAHHARUN, mai tsarkake waninsa; SAYYIDU, shugaba; HADI, mai shiryarwa; MUNILUL BASHA’IRI, mai bayar da bushara. YA kA’IDAL GURRI, ya jagoran masu hasken Arwala; ALMUHAIMINA, mai kiyaye addini da al’ummarsa; SADIkAN, mai gaskiya abun gasgatawa; HABIBAN, SHAHIDAN, MUNZIRAN, mai gargadi kar ayi da nasa ni a ranar Alkiyama.
Ya Ubangiji ka yi rahama ga wannan kadimi, mai kankan da kai, wanda ayyukansa suka baci. ABAL kASIM, MANSURA, Ya fiyayyen mahalarci acikin zuciyar masoyi (BARHAMA INYASS).
Cewa, kaine abin gasgatawa, MASDUkU; mafificin masu ceto, MUSHAFFA’IN; yana da daraja fiye da duk sauran shugabannin na daga Annabawa.
Ina ganinka ya Rasulullah, kai ne mai wasila da fadila, a Alkausara kuwa, kai ne mai shayarwa.
Ina rokon Ubangiji ya dauke damuwoyinmu, albarkar manzon Allah SAW, mafi girman masu daure Karaya (JABIRI). HAMIDUN, mai yabon kansa ne ko kuma abun yabo. Yana da Rawani, da safar fata, da hadimai masu yi masa aiki, mai tsarkakakken sirri ne, ya hau abubuwan hawa (Rakumi, Doki, Alfadari, Jaki). MUkAFFAN; kuma yana da takalma, yana rike sanda, yana da zobe, a hannun dama wata rana dama da hagu.
HUDAN, mai shiryar da halitta ne; ZA IZZATIN, mai madaukakiyar daraja; ZA MAKANATIN, mai madaukakiyar matsayi, ya dogara ga Allah matuka, shi ne HIMYAdA, mai kare alfarma; ma’abocin basira.
Allah ya yi wadaren wanda zai hana masoya su taru don nuna soyayyar Manzon Allah SAW, Allah ya jikan masoyi ranar da za a binciki ayyuka (ranar Alkiyama).
Tsira da amincin Allah su tabbata ga masoyinsa, MUSTAFA, MUKTARI, salati ne wanda da shi za a shafe dukkan laufuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp