Rundunar ƴ ansandan Jihar Katsina ta kama wani mutum mai suna Mubarak Bello, mai shekaru 38, daga unguwar Kofar Yamma a Ƙaramar Hukumar Kurfi, bisa zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba tare da kuma yin sojan gona.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiƙ, ya fitar a Katsina.
- Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita
- Abin Fashewa Ya Tarwatse A Masana’antar Ƙera Makamai Ta Sojojin Nijeriya A Kaduna
A cewar sanarwar: “Rundunar ƴ ansanda ta Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin CP Bello Shehu, ta yi nasarar cafke wani wanda ake zargi da laifin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma yin sojan, tare da ƙwato muhimman abubuwa daga hannunsa.”
“A ranar 13 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na dare, yayin aikin sintiri na yau da kullum, jami’an da ke cikin sashen ayyuka na rundunar sun samu nasarar cafke Mubarak Bello, namiji, mai shekaru 38, daga unguwar Kofar Yamma, Kurfi LGA, Jihar Katsina, bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma yin bogi.
“Ƙungiyar jami’an tsaro, bisa ƙarin kula da dabarun tsaron zamani, ta dakatar da wata motar Toyota Corolla, launin toka, mai lambar rijista Lagos GGE 473 BH, wacce wanda ake zargi ya ke tuƙawa. Bayan an yi masa tambayoyi, bai iya bayar da cikakken bayani kan kansa ko motar ba, lamarin da ya sa aka gudanar da bincike nan take.
“A yayin binciken motar, an samu waɗannan abubuwa daga hannun wanda ake zargin: bindiga ta gida guda ɗaya, harsashi guda huɗu, harsashi biyu da aka harba a baya, katin shaida na ƴ an sanda na bogi, da kuma ƙarin lambar rijistar mota ta (Kano FGE 68).”
“Wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin dalilan mallakar bindiga, katin shaida na bogi, da sauran abubuwan da aka kama daga gare shi.”
“Ƙungiyar jami’an tsaro, bisa ƙarin lura da dabarun tsaron zamani, ta dakatar da wani motar Toyota Corolla, launin toka, mai lambar rijista Lagos GGE 473 BH, wanda wanda ake zargi ya ke tukawa. Bayan an yi masa tambayoyi, bai iya bayar da cikakken bayani kan kansa ko motar ba, lamarin da ya sa aka gudanar da bincike nan take.
“A yayin binciken motar, an samu waɗannan abubuwa daga hannun wanda ake zargin: bindiga ta gida guda ɗaya, harsashi guda huɗu, harsashi biyu da aka harba a baya, katin shaida na ƴ an sanda na bogi, da kuma lambar rijista ta ƙari (Kano FGE 68).”
“Wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin dalilan mallakar bindiga, katin shaida na bogi, da sauran abubuwan da aka kama daga gare shi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp